Daga Kamal Yahaya Zakaria
Dan takarar majalisar tarayya a kananan Hukumomin kura madobi da garun Mallam a jam’iyyar APC Hon. (Dr) Musa Iliyasu Kwankwaso yayi Zargin cewa akwai kyakyawan yakinin Engr. Rabi’u Musa Kwankwaso zai janye daga takarar shugaban kasa da yake yi jam’iyyar NNPP ya kuma marawa dan takarar APC Asiwaju Bola Ahmad Tinubu.
Musa Iliyasu Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin da yake ganawa da masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC a karamar hukumar kura, a kokarin sa na tunkarar zabukan shekara ta 2023.
Yace alamu na cigaba da nuna cewa Sanata Kwankwaso zai hakura da takarar sa ya marawa dan takarar shugaban kasa na APC baya , saboda abun da ya kirawo bazai iya yin takarar ba.
” Irin wannan abubuwan da na gano tun tuni shi sanata Malam Ibrahim Shekarau ya gani yasa ya fice daga jam’iyyar NNPP ya koma jam’iyyar PDP, Kuma Ina tabbatar muku idan zaben ya mazo zaku gani”. Musa Iliyasu Kwankwaso
Musa Iliyasu Kwankwaso yace rashin tabbacin yin takarar Kwankwaso da wasu matsaloli Masu yawa ne yasa kullam yan kwankwasiyya suke ficewa daga tsarin suke komawa jam’iyyar APC.
A yayin taron Hon. Musa Iliyasu Kwankwaso ya karbi matasa maza da mata yan kwankwasiyya Yan social media wadanda suka ce sun ajiye tafiyar kwankwasiyya sun rungumi tafiyar jam’iyyar APC.
Zainab Husaini madobi ita ce ta yi magana a madadin matasan da yawansu ya haura 30, ta ce zasu bada duk gudunmawar da ake bukata domin ganin Musa Iliyasu Kwankwaso da sauran yan takarar APC sun yi nasara a zaben shekara ta 2023.
Kwankwaso dai shi ne jagora Kuma Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP a zabukan shekara ta 2023 dake tafem