Daga Kakaki
Sheikh Dr Yusuf Ali, Sarkin Malaman masarautar Gaya ya yi wannan furucin ne a lokacin da yake hira ta musamman da ‘yan jarida akan karramawar da Gidauniyar ‘Ganduje Foundation’ ta yi masa kan hidimar da yake yi wajen isar da sakon Allah (SAW).
Taron zantawa da ‘yan jaridar ya gudana ne a daren Juma’a 17/9/2022 a zawiyyarsa dake Unguwar Tudun Maliki a cikin birnin Kano inda ya samu halartar’ yan jaridu da kuma wasu muridan Shehin Malamin.
An karrama Shehin Malamin ne a yayin rufe musabakar Alkur’ani da Gidauniyar Ganduje take shiryawa a kowacce shekara.
Shehin Malamin ya jaddada cewa; “babu wata madogara yanzu a dukkanin al’ummar duniya baki daya, Musulmi da wadanda ba Musulmi ba illa wannan addinin, da kuma wannan littafin. Duk wadansu tsare-tsare da wadansu bincike-bincike da duk wani abu da za a gwada, an gwada, amma duniyarnan ga halin da ake ciki, haka take, sama da kasa, a birkice, ba a samu yadda ake so ba. Saboda haka babu wani wata fata ga al’ummar yanzu da wadanda za su zo nan gaba illa wannan addini da kuma wannan littafi”, ya tabbatar.
Ya kara da cewa; “duk wani bincike da aka yi a duniyarnan, komi zurfinsa, duk mamakinsa, duk sararin samaniyyar da aka tafi, duk kasar da aka tafi, duk abin da aka kirkiro, za ka samu Alkur’ani ya yi bayaninsa dalla-dalla. A bakin wa aka ji? A bakin Manzo Allah (SAW)”, ya nusasshe.
Ya lurantar da cewa ka da kawai a tsaya a karanta Alkur’ani, a ci gaba da zurfafa bincike, Alkur’anin zai warware dukkannin matsalolinmu baki daya, inji Shehin Malamin. “mu yi koyi da shi kamar yadda dabi’un Manzon Allah (SAW) da halayyarsa ya kasance Alkur’anin ne. Duk abin da Alkur’ani ya hana, ya hanu, duk abin da Alkur’ani ya ce ya yi shi ne yake yi. Ba abin da Alkur’ani ya bari”, ya tabbatar.
Malamin ya ce; “duk abin da za mu yi ya kasance Kur’ani shi ne zai kasance ya zama jagoranmu. Abin da ya ce mu yi shi ne za mu yi. Za a ga abubuwa sun rincabe baki daya. Saboda mene? Saboda wanda ya halicce mu ya ce ga abin da za a yi a cikin littafinsa na karshe, bama yi. Annabin da ya aiko na karshe babu wani Annabin bayanshi. Mune al’ummar karshe. Amma kuma ba ma bin abin da ya ce. Mu koma wannan littafi ga baki daya, ya zama shi ne zai zame mana mizani a shugabancinmu, a mulkinmu, a sana’armu, a nomannu, a aurenmu, a tarbiyyarmu, a huldarmu da jama’a. Abin da ya shafi lafiyarmu, da abin da ya shafi duk wani hali na siyarmu da sauran su”, ya jaddada.
Shehin Malamin a wani bangare na bayaninsa ya kuma shaida cewa makasudin ba shi wannan lambar girmama shi ne; saboda hidimar da yake gudanarwa shekara da shekaru wajen daukaka addinin Musulunci tare da zaburarwa da karfafawa kan karatun Alkur’ani mai girma. Shehin Malamin ya ce yana godiya ga Allah ta’ala bisa shiriyar da shi da ya yi da littafin Alkur’ani mai girma.
Shaikh Dr Yusuf Ali har wala yau a wani bangare na bayaninsa ya ce; ba yau ne farkon ba shi kyauta da Gwamna Ganduje ya yi masa ba. Amma ya ce wannan ta sha bamban saboda an ba shi ne kan Alkur’ani.
Shehin Malamin har wala yau, ya mika godiyarsa ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje bisa wannan karammawar. Ya yi kira ga sauran gwamnoni da shugabanni a matakai daban-daban da su bunkasa addinin Musulunci da karfafawa masu kokarin haddace Alkur’ani guiwa.
Gidauniyar ta Ganduje ta kasance tana ilmantarwa da karfafawa mutane karatun Alkur’ani, da gina makarantu da masallatai tare da musuluntar da wadanda ba Musulmi ba.