An baiwa ‘yar arewa Sarautar Cheif a Masarautar su Obasanjo

Date:

Daga Abubakar Sale Ya’akub

 

Masarautar Erunmu Owu dake Abeokuta a Jihar Ogun taga zabi Hajiya Fanna Muhd Kawu, ta bata Sarautar Yaye Akinrunwa, domin kara samar da hadin kai tsakanin Yan Arewa da kudancin Najeriya.

 

Cheif Hajiya Fanna, ta kasance Mai taimako da jikan al’umma batare da nuna bambanci ba, Kuma tana kan gaba wajen sanin magungunan gargajiya dana addinin Islama.

 

Kazalika itace Sarkin yakin  Magani magani ta Jihar Kano Kuma Sarauniyar Shareefan Najeriya.

Talla

Cheif Hajiya Fanna Muhd, ta samu nasarar tsallake dukkan matakan da ake bukata a Masarautar Erunmu kafin baiwa kowane mutum sarauta.

 

A ranar 17 ga watan Satumbar shekarar 2022, Oluroko Abdul Waheed Ayoade , wato Oluroko na Masarautar Erunmu Owu ya nada Chief Hajiya Fanna Muhd Kawu, Sarautar “YeYe Akinrunwa,” Adaidai lokacin da Sarkin yake murnar cikarsa Shekara daya akan karagar mulki.

 

Dimbin Al’umma dake ciki da wajen Jihar Ogun suma halarci taron nadin Chief Fanna Muhd Kawu wannnan mukami, sannan ita kanta ta tafi da mutane 10.

Talla

 

Tawagar Sarkin Shareefai dake Legas da Ogun da Yan majalisarsu suka halarci taron wanda dimbin al’ummar Masarautar suka cika da murna ganin cewa Hajiya Fanna itace mace ta farko daga Arewacin Najeriya da aka taba baiwa Sarauta a Masarautar Erunmu Owu, kuma sarautace da suka bayyanata a matsayin macen da zata kawowa Masarautar alheri da cigaba.

 

Sarkin Masarautar Erunmu Owu, Oluroko Abdul Waheed Ayoade, yace Cheif Hajiya Fanna tana da nagarta wadda ta dace a bata wannnan sarauta, kuma tana da kwazo da tausayi da hidima ga Al’umma sannnan tana da ilimi da sani akan abubuawa irir iri.

 

Yace wadannan suna daga cikin kyawawan halayen da suka sanya Yan Majalisar Masarautar Erunmu Owu suka amince a bata wannnan sarauta, cikin wadanda suka yarda akwai Tsohon Shugaban Najeriya Cheif Olusegun Obasanjo GCFR da masu zaben Sarki su 8

wannnan biki ya Sanya Jama’a farinciki sabo da yadda Cheif Hajiya Fanna ta rika kokarin kyautatawa Mahalarta taron masu dimbin yawa.

‘Yan uwa da abokan arziki suka cigaba da Taya Cheif Fanna Muhd, samun wannnan sarauta mai girma da daraja.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...

Za mu karawa Limamai, Ladanai da Na’ibansu alawus na wata-wata – Shugaban Karamar hukumar Dala

Daga Sani Idris maiwaya   Shugaban karamar hukumar Dala Alhaji Suraj...