Daga Kamal Yahaya Zakaria
An gudanar da bikin yaye ‘yan banga 600 da gwamnatin jihar Katsina ta dauki nauyin horaswa
Taron yaye yan bangar dai ya gudana ne a sansanin jami’an tsaro na NSCDC dake birnin Katsina inda daman nan ne aka ba su horon.
Da yake jawabi a wurin taron, Gwamnan jihar Katsina, Rt Hon Aminu Bello Masari wanda Sakataren Gwamnatin jihar ta Katsina, Alhaji Muntari Lawal ya wakilta ya yabawa mutanen da suka nuna sha’awar su ta shiga aikin bangar domin su taimakawa al’ummar su.
Haka zalika, Gwamnan ya kuma sha alwashin cigaba da mayar da hankali wajen tabbatar da tsaron al’ummar jihar ta hanyar bayar da dukkan gudummuwa da goyon bayan da za’a bukata.
Gwamnan ya kara da cewa yanzu haka gwamnatin ta ware Naira biliyan 1 da miliyan 500 domin gudanar da ayyukan da suka shafi tsaron al’ummar jihar.
Tun da farko mai ba Gwamna shawara kan harkokin tsaro, Malam Ibrahim Katsina ya jinjinawa jami’an rundunar ta NSCDC bisa horon da suka ba yan bangar wanda yace zai taimaka sosai wajen shawo kan matsalar da ta addabi jihar Katsina.
Haka zalika Ibrahim Katsina ya bayyana cewa daga yanzu kam ba bu sauran sassauci daga gwamnati da al’ummar jihar Katsina ga yan bindiga tunda dai sun zabi yin fito-na-fito da su.
Mai ba Gwamna shawarar ya kuma bayyana cewa kawo yanzu gwamnatin ta horar da yan bangar 1,100 daga cikin mutane 3,000 da gwamnatin ta yi niyyar horarwa idan aka hada da wadannan 600 da aka yaye yau.
A jawaban su daban-daban, shugabannin hukumomin tsaron da suka magantu a yayin taron sun yaba da yadda shirin horaswar ya gudana cikin dan karamin lokaci kuma aka samu abunda ake so.
Abubuwan da suka gudana a wurin taron sun hada da atisaye da yan bangar suka gudanar wanda ya burge dukkan mahalarta taron.