Shirin KSADP zai kara samar da aiyukan da zasu inganta Noma da Kiwo a Kano

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar
 Shirin  bunkasa noma da kiwo na jihar Kano, KSADP, ya bayyana cewa ya bayar da Kwangilar gudanar da wasu muhimman aiyuka a wasu kananan Hukumomin jihar kano da kudin su yakai  N6,036,334,688. 66,.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labaran shirin Ameen K Yassar ya aikowa kadaura24 a daren juma’ar data gabata.
 Ayyukan sun hada da inganta noman rani mai fadin hekta 1,006  a shirin noman ruwa na Watari, karamar hukumar Bagwai da gina cibiyoyin tattara madara guda 40 a wurare  a kananan hukumomi 15 na jihar.
Talla
 Aikin samar da ababen more rayuwa na Watari zai ci kudi N4,539,501, 897.08 yayin da za a gina cibiyoyin tattara madara guda 40 za’a yi shi akan kudi Naira 1,496,832,791.58.
 Bankin raya Musulunci da Asusun bukaci Rayuw na, LLF ne za su bayar da kudade domin gudanar da ayyukan, a wani bangare na bunkasa noma, tabbatar da samar da abinci mai gina jiki tare da inganta samar da kudaden shiga ga kananan manoma da makiyaya.
 Yan kwangila takwas wanda suke yan jihar kano su ne zasu gudanar da Ayyukan, kuma za su fara aikin ne a watan Satumba, 2022 kuma a kammala su a watan Disamba, 2023.
 Ana hasashen zuba jarin zai yi tasiri ga dubban manoma da makiyaya, ta yadda zai farfado da tattalin arzikin Kano.
Talla
 Da yake jawabi jim kadan bayan rattaba hannu kan kwangilolin da ma’aikatar shari’a ta jihar Kano ta shirya, kodinetan shirin na jihar kano, KSADP, Ibrahim Garba Muhammad, ya ce taron wani muhimmin mataki ne na inganta harkar noma a kano.
 “Wadannan ayyukan da nan ba da jimawa ba wasu ayyuka za su biyo bayansu, tabbas za su kawo sauyi a cikin arzikin noma na Kano, kuma za su fitar da adadi mai yawa na mutanenmu daga kangin talauci”.
 Don haka ya bukaci ‘yan kwangilar da su rika ganin ayyukan a matsayin hidima ga al’umma ba wai kawai don su sami kudi ba, yana mai jaddada cewa ana sa ran su bi duk ka’idojin kwangila domin samar da ingantaccen aiki.
 Shima da yake tsokaci, Manajan Darakta na Hukumar KNARDA, Dakta Junaidu Yakubu Muhammad, ya gargadi ‘yan kwangilar da cewa su sani an samar da wani kwakkwaran tsarin sanya ido domin kula da ayyukansu, Kuma ya bada tabbacin za’a hukunta duk wanda ya karya ka’idojin yarjejeniyar da aka yi dasu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An dakatar da Shugaba da Sakataren kungiyar APC X Eagle forum

Kwamitin zartarwa na kungiyar APC X Eagle forum ya...

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...