Zamu yada aiyukan Gwamna Ganduje ka’in da na’in – Hon. Bashir Rufa’i Lawan

Date:

Daga Kamal Yakubu Ali

 

Sabon Babban mataimaki na  musamman ga  gwamnan kano a ma’aikatar yada labarai Hon Bashir Rufa’i Lawan, ya Sha alwashin cigaba da wayar da kan al’umma a game da ayyukan da Ganduje ke gudanarwa a lungu da sako na jihar kano.

 

Kadaura24 ta rawaito Bashir Rufa’i Lawan  ya bayyana haka ne a yayin da yake kama aiki a matsayin babban mataimaki na musamman a ma’aikatar yada labarai karkashin jagoranci malam Muhammad Garba mai taken SwiftKey a yau.

Talla

Yace a shirye yake wajan yada ayyukan da gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje yake gudanarwa domin cigaban alumma, a loko da sako dake fadin jahar nan, inda yace zai hada hannu da kafafen yada labarai  da kuma gudanarda da aiki tukuru bisa ka’idojin aikin, domin sanar da al’umma ayyukan cigaba da Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ke gudanarwa a fadin jihar nan.

Kaddara ce tasa na fara rawar gala – Tahir Fagge

Shima anasa jawabin Kwamishinan yada labarai malam Muhammad Garba ya bayyana Hon Bashir Rufa’i Lawan a matsayin jajirtaccen matashi, wanda ake bukata wajan hidimtawa al’umma, inda ya bukace shi da yayi amfani da kwarewar da yake da ita wajen samar da cigaba da wayar da kan matasa, kasancer matasa sune kashin bayan cigaban kowacce al’umma.

Talla

 

Ya kuma tabbatar masa da cewa a shirye yake domin bashi dukkannin gudunmawar da yake bukata wajan gudanar da ayyukansa.

 

Muhammad Garba ya bukaci daukacin ‘ya’yan jam’iyyar APC dake karamar hukumar birni dasu kara damara, da kuma hadin kai domin samun Nasarar jam’iyyar APC a zabukan dake Tafe na shekarar 2023 domin cigaba da hidimtawa al’umma karamar hukumar birni da kano baki daya.

Sai da Sha’aban Sharada ya Amince da dokokin mu kafin mu bashi takarar ADP – Amb. Tasi’u Abdulrahman

Shima Anasa bangaren shugaban karamar hukumar birni Hon Faizu Alfindiki ya godewa gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje, da kwamishinan yada labarai malam Muhammad Garba ya yi bisa sanya ya’yan karamar hukumar birni a cikin kunshin gwamnati jiha, Wanda yace hakan ya samu bisa jajircewar kwamishinan yada labarai malam Muhammad Garba.

Alumma da damane suka raka Sabon babban mataimakin domin kama aika   wadanda suka hadarda shugabanin  jamiyya Apc na Karamar hukumar Birni da yan uwa da Abokanan arziki.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Sarkin Kano na 15 ya gana da Shugaba Tinubu kan rikicin Rimin Zakara

    Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado...

Da dumi-dumi: Tinubu ya baiwa sakataren jam’iyyar APC na Kano mukami

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Sakataren jam’iyyar APC na jihar Kano,...

Gwamnatin Kano ta haramtawa yan kwangila zuwa ma’aikatar kananan hukumomi ta jihar – Kwamishina

Gwamnatin kano ta ja kunnen yan kwangilar ayyukan kananan...

Iftila’i: Almajirai 17 sun kone kurmus 15, sun jikkata sanadiyya wata gobara

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Wata gobara da ta tashi ta...