Kaddara ce tasa na fara rawar gala – Tahir Fagge

Date:

Daga Aisha Aliyu Umar

 

Dattijo a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Tahir Fagge, ya bayyana cewa rashin kudi ne ya same shi, ga rashin lafiya, shi ya sa da aka neme shi aka bashi kudi ya je ya yi rawa a gidan Gala domin yiwa kansa magani.

 

Cikin tattaunawa da sashen Hausa na BBC, Tahir Fagge yace mutane ba sa fahimtar kaddara, wacce duk arzikin mutum ko taikaicinsa ba wuce kaddarar Rayuwa ta same shi ba, domin yace ya kasance yana fama da ciwon zuciya, kuma ba shu da kudin magani.

 

“A lokacin, idan na yi wa Ali Nuhu magana zai ba ni kudin, amma sai na ji kunya.

 

Talla

“Dama da farko shi ne ya ga wata waya a hannuna, sai ya ce ba zai yiwu ba, suna da rai ina rike irin wannan wayar, sai ya yi waya aka kawo min wata.

 

“To wayar na sayar na sayi magani; Sai na ji nauyin in sake komawa.

 

“Lokacin da nake bukatar kudi Naira 265,000, na je wajen Rarara ya ban dubu 20. Maishadda ya ba ni dubu 20, sai Abdul Amart ya ba ni dubu 15.

Talla

 

“Ina cikin wannan yanayi ne sai yaran nan (’Yan gidan gala) suka zo suka same ni suka ce sun sanya sunana a matsayin babban bako, za a bude gidan wasa. Nan take suka ba ni dubu N150,000.

 

“Da na je, ina zaune, sai suka ce akwai wakar Bazar Kowa wadda Lilisco ya hau, sai suka ce don Allah in hau in kwatanta wa yaran saboda ba su san wakar ba.

 

“Shi ne na hau wakar, sai kuma aka sa wata ta Hamisu Breaker, shi ne fa aka rika yada bidiyoyin nan,” in ji shi.

 

Tahir Fage ya ce ya yafe wa duk wadanda suka zage shi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Gwamnatin Kano ta yi karin haske kan batun goyo a babur

Gwamnatin jihar Kano ta ce masu sana’ar Achaba Kawai...

Kwamishinan shari’a na Kano ya gana da kwamishinan ’Yansanda kan korafe-korafen kama masu goyo a babur

Babban Lauyan Gwamnatin Kano kuma Kwamishinan Shari’a, Abdulkarim Kabiru...

Mai ciki ta mutu bayan ma’aikacin asibiti ya ƙi yarda a biya kuɗi ta waya

Wata mata mai ciki, Aisha Najamu, ta mutu a...

Kungiyoyin Arewa sun gargadi Tinubu kan shigo da Yakubu Dogara cikin Gwamnatinsa

Wasu kungiyoyin matasa da na zamantakewa-siyasa daga Arewa maso...