Faduwar Kwale-Kwale: An gano Gawar Mutane 97 a Kebbi – Atiku Bagudu

Date:

Gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi da ke arewacin Najeriya ya ce an gano gawar mutum 97 jumilla na waɗanda jirgin ruwa ya kife da su a garin Warrah na Ƙaramar Hukumar Ngaski da ke jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a Birnin Kebbi lokacin da yake karɓar baƙuncin ‘yan Majalisar Wakilan Najeriya da suka je yi masa ta’aziyya game da hatsarin, kamar yadda kamfanin labarai na NAN ya ruwaito.

Sakataren Gwamnati Babale Umar-Yauri wanda ya wakilci gwamnan, ya ce an binne mutanen yayin da aka ceto mutum 22 da ransu.

Tun a ranar 2 ga watan Yuni jirgin ya kife da fasinjojin cikinsa bayan ya taso daga Minna a Jihar Neja ɗauke da ‘yan kasuwa da masu haƙar ma’adanai, inda ya halaka mutum kusan 100.

46 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta Kano ta zabi sabbin shugabanninta

Kungiyar shugabannin kafafen yada labarai ta jihar Kano ta...

Al’ummar Kano ku baiwa AA Zaura hadin Kai domin ya kawo karshen fadan Daba – Baba Yawale

Daga Halima Umar Dogo   Babban Hadimin AA Zaura Alhaji Baba...

Gwamnatin Kano ta magantu kan Hukuncin kotu na zaben kananan hukumomi

Daga Khadija Abdullahi Aliyu   Gwamnatin jihar Kano ta bayyana farin...