Daga Rukayya Abdullahi Maida
Hukumar kula da kafafen yada labarai ta kasa NBC ta haramta sanya wakar Ado Gwanja ta WARR a gidajen Radiyo da Talabijin na kasar nan.
Hakan na dauke ne cikin wata Sanarwa da hukumar ta fitar mai kwanan watan 06 ga watan Satumba 2022.
Kadaura24 ta rawaito wakar ” Warr ” na daya daga cikin manyan wakokin mawakin wadanda suka shahara a wannan musamman a wajen mata.
Sanarwar da tace an dakatar da sanya wakar ne a radio da Talabijin Saboda wasu kalamai da yake yi a cikin baitocin wakar ta Warr wadanda suka Saba da dokokin hukumar da Kuma al’adar Hausawa.
” Wasu baitoci cikin wakar Warr wadanda suka hadar da :
” ….kafin a San mu ai mun ci kasahin uban mu…
“….zani zo bari insha fa hoda, ko kin zo da hodar ki uban ki zan ci warr…
“… Kowa yace zai hana ni uban sa zan ci..
Sanarwar tace wadannan baitoci da suke cikin wakar ta Warr sun sabawa sashin na 3, 18, 2c na hukumar dake kula da kafafen yada labarai ta kasa NBC.
Sabawa wannan umarni na hukumar NBC ga kafafen yada labarai na Radio da Talabijin zai iya sanyawa a hukunta kafar yada labaran.