2021:Yau ce Ranar Muhalli ta Duniya

Date:

Daga Sani Magaji Garko

Ranar 5 ga watan Yunin kowacce shekara itace ranar da majalisar dinkin duniya ta ware a matsayin ranar kula da Muhalli ta Duniya.

Ranar tana mayar da hankali wajen yayata matsalolin da suke barazana ga Muhalli domin yaki da gurbacewar Muhalli.

An fara murnar ranar ne a shekarar 1972 domin samar da tsare-tsaren cigaban Muhalli.

A lokuta da dama ana samun wasu ayyuka da suke kawo gurbacewar Muhalli Wanda hakan ke kawo nakasu a kokarin da akeyi.

Kididdiga ta nuna cewa a duk dikiku uku ana rasa filayen kula da Muhalli Wanda ake gina filayen wasanni da sauran wasu gine-gine.

Ranar ta na Kuma mayar da hankali wajen wayar da kan al’umma game da muhimmancin aiki tare da nufin kula da Muhalli ga rayuwar al’umma.

Tana kuma Kuma mayar da hankali wajen samar da tsare-tsare da nufin kawo karshen barazar da Muhalli ke fuskanta baya ga yin aiki tukuru da nufin farfado muhali da kare kwararowar hamada.

Bullar cutar Korona ta sake futar da barazar da Muhalli ke fuskanta inda bincike ya nuna cewa kaso 80 cikin 100 na gurbataccen ruwansha Yana komawa koramai da dam-dam Wanda hakan ke barazana ga dabbobin ruwa.

Gwamnatin jihar Kano karkashin jagorancin Gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ta ce tana daukar dukkan matakai da nufin yaki da matsalolin Muhalli.

Gwamnatin ta bakin kwamishinan Muhalli na jihar Kano Dakta Kabiru Ibrahim Getso ya ce e ta shiga Shirin kawata Muhalli Wanda hakan ke samar da kudaden ga gwanatoci da kuma shuka tsirrai.

Dakta Kabiru Getso ya ce nan da karshen disambar 2021 da muke ciki Gwamnatin jihar Kano zata shuka bishiyu guda miliyan daya.

Dakta Kabiru Getso ya ce za Kuma su gudanar da ayyukan gina Magudanan ruwa da gyara wadanda suka lalace da nufin yaki da zaizayar kasa da kuma gurbacewar yanayi.

Taken taron na bana shine farfado da yanayin tsarin halittu Wanda ya mayar da hankali wajen fito da matsalolin shuka tsirrai da kawata birane da bishiyoyi da kuma yashe Magudanan ruwa.

362 COMMENTS

  1. Усик затролив Джошуа перед чемпіонською супербитвою “Підозрюю, що він кращий, ніж здається”: Ф’юрі “викрив” хитрий план Усика на бій із Джошуа “Усик, можливо, йде другим”: Джошуа назвав Энтони Джошуа Александр Усик 6. Протистояння Усик-Джошуа – поширені питання 6.1 . Пряму трансляцію поєдинку між Усиком та Джошуа можна подивитись на телеканалі megogo попередньо сплативши суму від 29 до 99 гривень, або ж на сайтах таких провідних БК як

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...