Daga Isa Ahmad Getso
Wani matashi dan shekara 25 mai suna Ammar Ibrahim ya nutse a wani kogi a kauyen Tattarawa da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar kashe gobara ta jihar Saminu Abdullahi ya fitar a yau Laraba a Kano.
Abdullahi ya ce lamarin ya faru ne a jiya Talata .
“Mun samu kiran gaggawa da misalin karfe 11:34 na safe daga wani Muhammad Sani kuma mun aika da tawagar mu zuwa wurin da abin ya faru da misalin karfe 11:55 na safe.
“Direban adaidaitasahu din da ke kan hanyarsa ta komawa Kano, ya yi fakin a gefen titi kusa da wani kogi da nufin wanke babur din, amma sai tsautsayi ya ja shi cikin kogin.
“Ya yi ƙoƙari da yawa don ya tsere amma hakan bai yiwu ba,” in ji Abdullahi.
Ya ce an fito da marigayi Ibrahim daga cikin ruwan a sume kuma daga baya aka tabbatar da rasuwarsa.
Abdullahi ya ce an mika gawar ga Sifeto Jerry Mathew na ofishin ‘yan sanda na Dawakin Tofa.