Daga Rukayya Abdullahi Maida
Hirar da tsohowar jarumar fim din kwana chasa’in na Arewa24 Safara’u wacce bayan ta fara waka ta koma Saffa ta yi da sashin Hausa na BBC ta janyo cheche-kuche a tsakanin mata musamman a kafafen sada zumunta na social media.
A jiya litinin a Hirar da tayi da BBC Hausa saffa bayan an tambaye ta yadda ta ji game da fitar bidiyon tsaraicinta , sai ta ce ta damu sosai Inda har sai da ta kai ko wajen bata fita saboda gudun tsangwamar da Zata fiskanta.
Wasu Magoya bayan Shekarau da suka shiga NNPP tare sun jaddada goyon bayan su ga Kwankwaso
Babban abun da ya jawo cheche-kuchen shi ne da tace “kowacce mace tana yin hoto ko bidiyon tsaraicinta ta bar shi a wayarta saboda da nishadi”.

Wannan kalamai basu yiwa mata da yawa a shafukan sada zumunta dadi ba, hakan tasa suke ta mayar mata da martani wasunsu ma har da zagi saboda abun da suka kirawo bata musu suna da ta yi.
Baya ga mata maza ma sun shiga cikin Masu yin Allah Wadai da Wadancan kalamai na jaruma Safara’u wacce yanzu aka fi saninta da suna Saffa.
Dama dai Safiyar Yusuf wato saffa tana shan suka kan yadda take gudanar da harkokin wakokinta cikin Rashin bin tsarin al’adun Hausawa da Kuma sabawa addinin musulunci ta hanyar kalamai da Kuma shigar da take yi.
Idan za’a iya tunawa kadaura24 ta rawaito Hukumar tace fina-fina ta jihar kano ta aiyana Neman mawakiyar saboda korafe-korafen da hukumar ta karba daga al’ummar jihar kano na rashin mutunta al’adun mutane kano a cikin wakokin Saffa.