Ambaliyar ruwa: Gwamnatin Kano za ta rushe gine-gine da a ka yi kan hanyoyin ruwa

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Gwamnatin Kano ta ce ta kafa wani kwamiti da zai gaggauta yin nazari da magance yawan ambaliyar ruwa da ruwan sama ke haifar wa a jihar.

 

Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Muhammad Garba ne ya bayyana hakan a wata sanarwar da ya fitar a jiya Litinin a Kano.

 

Ya ce gwamnati ta damu da irin ambaliyar ruwan da ke faruwa a jihar, musamman a cikin birni.

 

Ya ce kwamitin zai ɗauki nauyin duba titina, kwatoci da kwalbati da su ka lalace kuma su ke toshe magudnan ruwa domin a gyara, ko kuma a gina sababbi.

 

Ya ƙara da cewa kwamitin zai bi duk wasu gine-gine da a ka yi a kan hanyoyin ruwa da su ke haifar da ambaliya domin rushe su.

 

Kwamishinan ya kuma nuna rashin jin dadin da kuma jajanta wa waɗanda ibtila’in mabakiyar ruwan ya shafa.

 

Garba ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su kwantar da hankalinsu domin gwamnati za ta tashi tsaye wajen kawo ƙarshen matsalar cikin lokaci kankani.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...