Daga Rukayya Abdullahi Maida
Hukumar zabe Mai zaman kanta ta kasa reshen jihar Kano (INEC) tayi kira ga Yan jaridu dasu kaucewa tsoro yayin dauko Rahotanni lokacin babban zabe mai zuwa na 2023.
Shugaban hukumar Barista Sulaiman Alkali shi ne yayi kiran yayin bitar yini guda da kungiyar Yan jaridu mata ta Kano (NAWOJ) ta shirya anan Kano domin fadar da su hanyoyin da zasu inganta aikinsu.
Sulaiman alkali ya kara da cewa yan jarida na cikin masu ruwa da tsaki a dukkanin harkokin zabe a Nigeria don haka yace akwai bukatar su nuna kwarewa a kowane lokaci ba tare da son zuciya ba musamman a rahotannin su na zabe mai zuwa.
Kazalika yayi kira ga yan jaridu da su cigaba da wayar da kan jama’ar jihar Kano, muhimmancin karbar katin zabensu na dindin kasancewar akwai wadanda Blbasu karbi Katin, Kuma duk wanda bashi da kanti ba zai iya yin zabe ba, kamar yadda dokar zabe ta fada.
Anata jawabin Shugabar kwamitin mata Yan jaridu ta jihar kano Hajiya Hafsat Sani Usman ta ce sunyi tunanin shirya taron karawa juna sanin ne don inganta aikin da Kuma sabbin dabarun dauko Rahotanni a zabukan shekara ta 2023 ga ‘ya’yan kungiyar na jihar Kano.
“Mun yi Wannan hobbasa ne biyo bayan kwarin gwaiwar da kungiyar ta samu daga gwamnatin Kano, wadda take tallafa mana a koda yaushe idan bukatar hakan ta taso”.
Tace tana fata Yan jaridu mata a kana zasu cire tsoro dan bada ta tasu gudunmawar wajen dauko Rahotanni na gaskiya wanda hakan zai sa sami sahihi kuma amintaccen sakamakon zabe a shekara ta 2023.
A nasa bangaren kwamishinan yada labarai na jihar Kano Muhammad Garba yace sashi na 22 na kundin tsarin mulkin kasar nan, ya baiwa dan jarida damar shiga duk wani abun da ya shafi al’amuran al’umma. Wanda keda alaka da yada duk wasu labaran gwamnatin Kano, sha’anin aiki Bai bashi damar halartar Taron ba.
Kwamishinan wanda shugaban kungiyar yan jarida ta kasa reshen jihar Kano (NUJ) kwamared Abbas Ibrahim ya wakilta yace yana da yakin horon da yan jaridun mata suka Sami zasu aiwatar da shi a babban zabe mai zuwa, don sauke nauyin da Kundin Tsarin Mulkin Kasa ya dora musu .
Mr.chris Isiguazo, shi ne shugaban kungiyar yan jaridu ta kasa a yayin taron da mataimakinsa na musamman Ibrahim Garba ya wakilta yace sakatariyar kungiyar yan jaridu ta kasa ce ta bada umarnin shirya wannan taro a daidai wannan lokaci da ake shirye- shiryen gudanar da zaben shekarar 2023 a wannan kasa.
Isiguazo ya hori yan jaridu da su amfani da kwarewar da suke da ita wajen bin dokoki da ka’idojin aikin jarida don kare kimar aikin a idanun duniya.
Wakiliyar kadaura 24 ta rawaito cewa anyiwa taron take da “Mata yan jarida su ne manyan shedu a zaben 2023”, la’akari da gudunmawar da zasu bayar wajen bugawa da yada labarai yanda ya dace daga ofisoshin su na yada labarai anan Kano.