Ɗan takarar shugabancin kasa a inuwar sabuwar jam’iyya ta hamayya, NNPP, Rabi’u Musa Kwankwaso ya ce jam’iyyarsa za ta kwace mulki daga hannun gwamna Babagana Umara Zulum a zaɓen 2023.
Kwankwaso ya shaida hakan ne a birnin Maiduguri lokacin bude ofishinsu na kamfen a ranar Asabar.
Sanata Kwankwaso ya ce jam’iyyarsa ce za ta lashe zaɓe a Najeriya tun daga matakin jihohi har Tarayya.
Kallon Uba Nake Yiwa Rarara, Saboda Yadda Yake Kula da ni – Abubakar Maishadda
Sannan ya buƙaci magoya bayansa su kasa su kuma tsare kamar yada ya aiwatar a Kano a lokutan zaɓe.
Dole dan Kwangilar da ya Gina Gadar Lado ya Dawo ya gyara ta -Ministan aiyuka
BBC Hausa ta rawaito Kwankwaso ya je Maiduguri ne kwana biyu bayan hukumar raya birane ta jihar ta rufe ofishinsu kafin daga bisani gwamna Zulum ya umarci a sake buɗe ofishin.