Daga Auwal Alhassan Kademi
Dan takarar shugaba Najeriya a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce ba zai mika wa gwamnatocin jihohin kasar ragamar tafiyar da jami’o’in gwamnatin tarayya ba.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Paul Ibe, ya fitar ya ce sun lura cewa an juya maganar da dan takarar shugaban kasar na PDP ya yi a wajen wani babban taro na kungiyar lauyoyin Najeriya da ya gudana a Legas a kan batun da ya shafi bangaren ilimi da hanyoyin da zai bi wajen warware matsalolin da bangaren ke fuskanta.
Wasu muhimman abubuwa da Shekarau ya fada game da matsyinsa a NNPP
Ya ce a cikin bayanan Atiku, bai ce zai mika ragamar kula da jami’in gwamnatin tarayya ga jihohi ba idan har aka zabe shi a zaben shugaban kasa mai zuwa.
Wannan ba daidai ba ne don bai hadi haka ba a lokacin da yake bayar da amsa a kan tambayoyin da aka yi masa game da manufofinsa in ji shi.
Majalisar dokokin Kano ta amince da sabbin kwamishinonin da Ganduje zai naɗa
Ya ce abin da Atiku Abubkar yake nufi shi ne matakan da zai bi daki-daki na rage wa gwamnatin tarayya nauyin tafiyar da jami’on da ke karkashinta.
A don haka batun cewa zai mika wa gwamnatocin jihohi raga,ar tafiyar da jami’oi ba gaskiya ba ne.