Daga Safiyanu Dantala jobawa
An bukaci magoya bayan jam’iyar PDP a duk inda suke, da su hada kansu don cimma nasarar zabe mai zuwa na 2023 a kasar nan.
Mataimakin coordinator na neman zaben Atiku Abubakar Turakin Adamawa, Hon Abdullahi Maikano Chiromawa (Jarman-Garun malam) shi ne ya bukaci hakan, a lokacin da yake cigaba da ganawa da ‘ya’yan jam’yar PDP na jihar kano.

Ya ce duk wata nasara ba ta samuwa sai ana da da kyakkyawan hadin kai da amana a tsakanin magoya baya.
A Wannan karo MaiKano Chiromawa ya ya gana ne da ‘ya’yan kungiyar People’s Democratic Party National Youth Agenda PDP-NYA reshen jihar Kano tare da shugaban ATIKU/OKOWA UNIFIER PROJECTS Najib Nasir a ofishin tafiyar ATIKU/OKOWA 2023 dake Gyadi-Gyadi lan titin Zaria,Kano.
Kungiyar Kanam Media Hub ta horas da mata yan jaridu dabarun aiki a Kano
A karshe ya yi wa kungiyoyin tafiyar da alkawarin basu gudunmawarsa don cigabansu da al’ummar kasa baki daya matukar Wazirin Adamawa Atiku Abubakar ya lashe zaben shekara ta 2023 me zuwa.