Daga Isa Ahmad Getso
Gwamnan Jihar Kogi da ke tsakiyar Najeriya, Yahaya Bello, ya bayar da umarnin rufe gidajen karuwai a fadin jihar.
Kazalika ya haramta sanya takunkumai a bainar jama’a da zummar ganin cikakkiyar fuskar kowa domin magance matsalar tsaro.
Wannan umarni ya biyo bayan matsalolin tsaro da ake samu a wasu sassan jihar.

Gwamna Bello ya bayar da umarni ne ranar Talata a Lokoja yayin taro da sarakunan gargajiya na jhar.
Gwamnan ya bayar da umarnin rusa yankunan da ake kama-wuri-zauna da ke Lokoja, Osara, Zango, Itobe, Obajana, da wasu sassan jihar.