Daga Ibrahim Sani Gama
Shugabancin kungiyar kasuwar Singa ya bukaci Gwamnati ta tallafawa mata da suke gudanar da kasuwancinsu a kasuwar domin habaka kasuwancinsu da ci gaban tattalin arzikin jihar Kano.
Shugabar dake kula da al’amuran mata ta kungiyar kasuwar, Hajiya Maryam Musa Gawuna ce ta bukaci haka a wata tattaunawa da manema labarai a kasuwar ta Singa.

Maryam Gawuna ta ce tallafawa mata da jari a kasuwanci yana da mutukar mahimmanci saboda su sun iya ririta kudi ko ya yake, don haka idan aka tallafa hakan zai ingata rayuwar su da Kuma ciyar da tattalin arzikin jihar kano dana kasa gaba.
INEC ta rufe yiwa yan Nigeria rijistar katin zabe
Shugabar ta yi kira ga Gwamnatoci a dukkanin matakai, da su ci gaba da tallafawa mata da jari domin rage masu zaman kashe Wando da yawaitar talauci tsakanin al’umma.
Hajiya Maryam Gawuna, ta kuma yi kira ga mata da su daina raina kananan sana’o’i duba da cewa daga karamar sana’a ne, ake samun bunkasa ta zamo babba, inda tace yanzu lokaci ya canza an daina raina kananan sana’o’i ana gudanar da sana’o’in ne don rufawa kai asiri.
Shugaban K/H da Kansilolinsa sun fice daga PDP a jihar Sokoto
mata suna da rawar takawa a fannin harkokin kasuwanci da bunkasar tattalin arziki a kasar nan, shi ya sa kamata ya yi Gwamnatocin jihohi dana tarayya su yi duk mai yiyuwa domin ganin sun tallafawa mata da jarin da za su rike kansu da iyalansu”. Inji Maryam Gawuna
Daga karshe ta yi kira ga yankasuwa da masu hannu da shuni da su rika saukakawa a kayayyakinsu da zarar, sun samesu a cikin sauki domin al’umma su ji dadin gudanar da rayuwa cikin sauki.