‘Yan Sanda Sun ce Ahmad Gulak Bai Sanar da su ba kafin ya fito daga Otel

Date:

Daga Halima A Musa

Rundunar ‘yan sanda ta Kasa reshen jihar Imo ta ce an kashe Ahmed Gulak, wani jigo a jam’iyyar APC a kusa da tashar jirgin sama a Owerri, babban birnin jihar.

 Jaridar TheCable ta ruwaito cewa an harbe tsohon mai taimakawa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a daren ranar Asabar yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama don tafiya Abuja.


 A cewar ‘yan sanda, Gulak ya bar otal dinsa ba tare da wani cikakken tsaro ba duk da rashin tsaron da ake fama dashi a jihar.


 Bala Elkana, mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda na Imo, ya ce‘ yan bindiga shida sun harbe jigon na APC wanda ke kan hanyarsa ta zuwa filin jirgin sama a cikin motar haya.

 Sanarwar ta ce: “A ranar 30/5/2021, da misalin karfe 07: 20hrs,‘ yan bundiga sun tare kuma sun kai hari kan wata motar Toyota Camry dauke da Ahmed Gulak da wasu mutum biyu wadanda ke kan hanyarsu ta zuwa Filin jirgin Sam Mbakwe don yin jirgi.


 “Ahmed Gulak ya bar dakinsa na otal din Protea ba tare da ya sanar da‘ yan sanda  ba Kafin ya fita saboda yanayin tabarbarewar tsaro a Kudu maso Gabas musamman jihar Imo.


 “Ya tafi ba tare da rakiyar jami’an tsaro ba, yayin da direban tasi din ya bi hanyar da ba ta dace ba zuwa filin jirgin, wasu‘ yan Bindiga shida wadanda ke tafiya a cikin wata Toyota Sienna sukaharbe su Ahmed Gulak a kusa da Umueze Obiangwu a karamar hukumar Ngor-Okpala kusa da  Filin jirgin sama.

 “Kwamishinan ‘yan sanda na Imo CP Abutu Yaro, fdc ya ba da umarnin gudanar da bincike cikin tsanaki ,kuna an tura runduna ta musamman da za ta zagaye yankin tare da cafke masu laifin.”


 Kungiyar Masu Da’ar neman yankin Biafra (IPOB) ta bayar da umarnin zama a gida ga mazauna jihohin kudu maso gabas daga 29 zuwa 31 ga Mayu.


 Sakamakon wannan umarni, ana ganin tattalin arziki yankin Zai shiga Wani hali Saboda yadda mazauna garin suka zabi zama na Zama a gida saboda tsoron rasa Rayukansu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...