Gwamnatin Kano Ta Tabbatar da Kara Inganta Ilimi, Lafiyar Yara a Kano

Date:

Daga Abdulmajid Habib Isa Tukuntawa

 Gwamnatin jihar Kano ta sake nanata Kudirinsta don Kara Daga darajar ilimi, kiwon lafiya da zamantakewar yara.


 Gwamnan jihar Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan yayin bikin zagayowar ranar yara ta duniya, wanda aka gudanar a gidan gwamnati na Kano.


 Ya bayyana cewa gwamnatin jihar kano za ta ci gaba da bai wa ranar yara ta duniya muhimmanci sosai kuma za ta ci gaba da fito da ayyukan ci gaba don inganta rayuwar yaran.


 “Yau ce ranar ku, hakkin mu ne mu sanya ku cikin farin ciki ta hanyar ci gaban yara mai ɗorewa.  Ina mai farin cikin kasancewa tare da ku a yau kasancewar taron ya tara yara, mutane masu buƙatu ta musamman da marayu ” inji Ganduje


 Dakta Ganduje ya kara da cewa wannan mummunar cutar ta 19 ta yi sanadiyyar mutuwar mutane da yawa a kano saboda haka hakkin gwamnati ne ta kula da yaran da suka rasa iyayensu.


 A nata jawabin mai dakin gwamnan  Kano, Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ta bayyana taken ranar yara ta duniya ta bana da cewa an zabi taken Daya dace da yanayin da ake ciki.


 “Gwamnatin jihar Kano ta samar Shirin ilimi kyauta kuma tilas, gwargwadon yadda yaro zai samu ilimi sosai zai taimaka wa ci gaban al’umma”.


 Tun da farki, kwamishiniyar harkokin mata da ci gaban al’umma ta jihar kano, Dokta Zahra’u Muhammad Umar ta bayyana ranar yara ta duniya a matsayin wata hanya ta yin la’akari da zamantakewar yara da iliminsu.


 Tace ta lura da cewa wannan annoba ta shafi yara a duniya baki daya kuma idan ba a magance su akan lokaci ba zai haifar da matsala ga rayuwar yara.


 ‘Ina mai farin cikin yi  Muku maraba da zuwa wannan taron na tarihi, wanda rana ce ta nuna kauna da jajircewa ga yaran mu ababen kaunarmu”. Dr. Zahra’u


 Ranar yara ta duniya ta 2021 mai taken “Tasirin Covid-19 akan lafiyar yaran Najeriya: Hanyar ci gaba” an yi bikin a Kano tare da wasan kwaikwayo, raye-rayen al’adu, nishaɗi da dai sauransu.

108 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Da dumi-dumi Dangote ya sake rage farashin man fetur a Nigeria

Daga Rahama Umar Kwaru   Matatar mai ta Dangote ta bayyana...

Akwai bukatar kebe rana ta musamman a matsayin ranar tsofaffin dalibai a Kano – Kwamared Waiya

Kwamishinan yada labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim...

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...