Ya kamata Gwamnati ta hana Fina-finan da ake kwacen waya a cikinsu – Wata kungiya

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Wata kungiya dake ragin yaki da matsalar kwacen waya a jihar Kano ta bukaci  gwamnati da majalisar dokokin jahar kano data ayyana masu amfani da makami suna kwacen waya amatsayin Yan fashi da makami, tare da zartar musu da hukunchi dai-dai da Yan fashi da makami kamar yanda doka ta tanada a tsarin dokokin jahar kano da kasa Baki daya.

Shugaban kungiyar Abdulwahab sa’id Ahmad ne ya bayyana hakan a cikin wata takarar bayan taro da shugaban sashin yada labaran kungiyar Aminu Abba Kwaru ya sanyawa hannu kuma ya aikowa kadaura24.

Sanarwar ta kuma kara da cewa  gwamnati ta umarchi hukumar tace fina finai ta jahar kano, data dakatar da masu shirya fina finan hausa a jahar daga shirya fina finan masu nuna yanda ake ta’addanchi da gurbata tarbiya. Domin irin Wannan fina finan suna taka muhimmiyar rawa wajan gurbata tarbiyar matasa da kuma nuna dabarun kwacen waya da sauran laifuka.

2. A wani bangaren kuma kungiyar tayi kira Ga majalisar malamai da limamai ta jahar kano suci gaba da wayarwa da jamaa Kai akan hakkin bawa yara tarbiya a musulunchi da kuma hukunchin da ubangiji ya tanada Ga duk uban daya bada gudunmawa wajan lalacewar tarbiyar ‘yayansa. ta hanyar amfani da mambarin jumaa da majalisin karatuttuka.

3. Shugaban kuma yayi kira ga masarautar jahar kano data umarchi hakimai, dagatai da masu unguwanni da Lallai su samar da kwamitin tsaro Acikin dukkan unguwannin jahar kano domin taimakawa jamian tsaro da bayanan sirri.

4. Daga cikin jan hankalin da kungiyar tayi taja hankalin kafafan yada labarai dake jahar kano, dasu samar da shirye shirye na musamman domin wayarwa da alumma Kai da dabarun kare Kai domin samun nasarar dakile Wannan annobar ta kwacen waya a jahar kano.

5. Daga karshe shugaban kungiyar Abdulhawab said Ahmad yaja hankalin Yan siyasa da suji tsoron Allah akan gudunmawar da suke bayarwa wajan dakile hukuma na samar da hukunchi akan masu aikata laifuka, acewar shugaban yin hakan babban koma bayane Ga tarbiya da tsaron Wannan jaha tamu me albarka.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika sakon ta’aziyyar Rasuwar Aminu Dantata

Daga Sadiya Ahmad   Kungiyar Farfado da martabar Arewa ta Mika...

Kungiyar ’Yan Jaridun Kano Arewa ta Aike da Sakon Ta’aziyyar Rasuwar Alhaji Aminu Dantata

  Kungiyar ’Yan Jarida ta Kano Arewa ta bayyana alhinin...

Ku na da rawar takawa wajen inganta Lafiyar al’ummar Kano – Waiya ga jami’an yada labarai

Daga Abubakar Sayeed Kwamishinan Ma'aikatar yada labarai da harkokin cikin...

Ana daf da yin jana’izar Aminu Dantata a Madina

Tawagar da gwamnatin Najeriya ta tura zuwa Madina na...