Matsayin Hukumar Alhazai ta Kano akan batun Mutane Dubu 60 da zasu sauke farali a bana

Date:

Abubakar Sadeeq

Hukumar Jin Dadin alhazai ta jihar Kano ta Bukaci Maniyata Aikin Hajjin bana dama Sauran al’ummar jihar nan dasu kwantar da hankalinsu game da sanarwar adadin wadanda aka ce zasu sauke farali a bana.

Shugaban Hukumar Alhaji Muhd Abba Danbatta ne ya bayyana hakan Yayin daya zanta da Manema labarai a ofishin sa dake nan Kano.

Alh. Muhd Abba yace batun Mutane Dubu 60 da Hukumar lafiya ta Kasar Saudiyya tace zasu yi aikin Hajjin bana shawarace ta bayar bawai shi ne Karshen Maganar ba.

Kadaura24 ta rawaito cewa Yace Ita Hukumar lafiya ta Kasar Mai tsarkin ta bada shawarar ne Matsayin su na Masana harkokin Lafiya Saboda yadda za’a tabbatar anbi ka’idojin kare Kai Daga Annubar Corona.

Alhaji Muhd Abba Danbatta ya Kara da cewa Har yanzu Matsayin su na Hukuma ba’a aiko musu da Wata sanarwa ba Daga Hukumar kula da Aikin Hajji ta Kasa (Nahcon).

” Ina so Maniyata su Sani wancan labari da ya fita Shawara ce kawai Hukumar lafiya ta bayar za’a iya amfani da ita zaku a iya ajiyeta ,kawai abun da muke Bukata Daga Maniyata shi ne su dage da yin addu’oi Kuma su cigaba da zuwa bita”. Inji Muhd Abba Danbatta

Muhd Abba Danbatta yace akwai kasashen da Kasar Saudiyya ta Hana su zuwa Kasa domin gudanar da aikin Hajji da umara Amma yace Nigeria Bata cikinsu.

” Kasashen sune Indonesia,Bangaladash, England, Germany, Malesia ,Turkey da dai sauransu to Amma Kasar mu Nigeria Bata cikinsu ,Kuma Dama Nigeria ce ta biya a yawan kasashen Masu zuwa Aikin Hajji a Duniya”.

Shugaban Hukumar Jin Dadin alhazan ta jihar Kano Alhaji Muhd Abba Danbatta ya bukaci al’ummar jihar Kano dasu dage da yin addu’oin Allah ya magance Annubar Corona data addabi Duniya.

1 COMMENT

  1. Maganar gaskiya a mayarwa da jama’a kudaden su domin akwai wadanda tun shrkarar suka ajiye kudinsu yanzu su yakamta abawa damar tafiya wandanda suka biya a bana kuwa abasu kudin su ku suma sujira badi idan Allah ya kaimu tun lamarin yazama yahudanci kasar saudiya ta daukowa kanta talan turmi. Tunda tsarin yahudanci ya shiga zukatan shuwagabanni ta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Bayan shekaru 20, Kotun Ƙoli ta sanya ranar yanke hukunci kan rikicin masarautar Gwandu

Kotun Koli ta sanya ranar yanke hukunci kan daukaka...

Hukumar Shari’ah ta kaddamar da kwamatoci domin kawo sauye-sauye game da cigaban Shari’a a jihar Kano

  Hukumar Shari'ah ta jihar Kano karkashin jagorancin mukaddashin shugabanta...

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...