Fadar Shugaban Ƙasa ta musanta labarin da ke cewa shugaba Muhammad Buhari ya goyi bayan guda daga cikin masu neman takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC.
Mai magana da yawun shugaban, Malam Garba Shehu ya bayyana haka a yau lahadi a wata sanarwar da ya fitar.
Ya ce sam–sam shugaban bashi da wani da ya ke so a matsayin dan takarar sa la’kari da yawan mutanen da suka nemi yiwa APC takarar shugabancin kasa a zaben na 2023.
Ya kara da cewa ba demokradiyya ba ce Buhari ya zabi mutum guda shi ka dai a matsayin wanda zai yi wa Jam’iyyar takara.
Sai dai ya ce shugaban na goyon bayan yin masalaha ne kasan cewar yin hakan ka’iya saukaka zaben cikin gida da Jam’iyyar ke shirin gudanarwa a makonnan da muke ciki.