Daga Rukayya Abdullahi Maida
Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari, ya nuna goyon bayansa ga mika takarar Shugaban kasa zuwa Kudu a 2023bcikin jam’iyyar APC.
Kadaura24 ta rawaito Ya bayyana hakan ne a wajen taron liyafar cin abincin dare da ta gudanar tare da masu neman tsayawa takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a Abuja.
Wata kila hakan ce tasa Gwamnan Jihar Jigawa Abubakar Badaru ya janye daga takarar shugaban kasa da yake yi a jam’iyyar jam’iyyar APC.
Ya fice daga cikin Waɗanda zasu gudanar da zaben fidda gwanin da aka shirya yi ranar litinin bayan gwamnonin APC 10 sun goyi bayan a barwa Kudu yayi takarar Shugaban kasa a 2023 Cikin APC.
Haka zalika Rahotanni na tabbatar da cewa gwamnan Jihar Ebonyi David Umahi ya janyewa Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad lawan takarar sa.