Wani bincike ya gano shan madaidaicin shayi ko gahawa a kowacce rana na rage haɗarin mutuwa.
Wasu masana kimiyya na China da ke gudanar da binciken sun gano hakan bayan nazari kan mutum 170 a Burtaniya.
Bayan sake sauya yanayin rayuwarsu, masanan sun gano wadanda suke shan gahawa da sukari ko akasin haka, na rage hadarin mutuwar farat daya, idan aka kwatanta da wadanda ba sa shan shayi kwata-kwata.
Binciken ya kuma gano raguwar mutuwar da kashi 29 cikin 100, sai dai masanan sun ce ba wai an karkare binciken ba ne, za a ci gaba saboda wannan nazari na farko ne da aka fara.