A A Zaura ya musanta labarin yiwa Shekarau da Kwankwaso ritaya a Siyasa

Date:

JAN HANKALI!!!

BABU INDA NACE ZANYIWA SHEKARAU DA KWANKWASO RITAYA

An jawo Hankali Kan wasu wallafe wallafe Dake zagayawa Yanzu haka a jaridun yanar gizo gizo, inda ake ikirarin nace, “zanyiwa Kwankwaso da Shekarau Ritaya”. Gaskiyar Magana itace Babu inda nace Haka, Hasalima na kirasu da iyayena I cikin hirar da ake dakko zancen.

Abinda nace a lokacinda Yan Jaridu suka tambayeni:” Yaya Kake ganin Fuskantar manyan jiga jigai guda 2, tsofaffin Gwamnoni, sanatoci Kuma tsoffin ministoci a wannan zabe na shekarar 2023?

Abinda nace shine, ” da yaddar Allah, ni zan Lashe zaben 2023, idan Allah ya bani, kaga sai Malam ibrahim Shekarau da Sanata Rabi’u Musa kwankwaso suje su huta, dukansu sunyi aiki tukuru a lokutansu, Kuma idan ka duba, zakaga sadda sukayi wannan kokarin sunada jini a jika, saboda haka wadannan iyayen nawa guda biyu zasuje su huta insha ALLAH a shekarar 2023″

Inaso Al’umma su sani cewa ban taba aibanta ko cin zarafin Koda sa’a naba, balle wanda nake Kallo a sa’oin iyayena Kuma nake kallonsu a iyaye. Ban taba daukar Siyasa a Batanci ba, Kuma ban yadda da Siyasar cin zarafi, Mutunci da Batanci ba. Muna Siyasa Kuma ta muntuntawa da Karramawa don cigaba.

Ina kira ga gidajen jaridun da suke yada wannan irin labaran kanzon kurege da suguji ayi amfani dasu don cimma burin Siyasa ganin cewa Hakan nada illa hatta a Shari’ance

Nagode.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

An dakatar da Shugaba da Sakataren kungiyar APC X Eagle forum

Kwamitin zartarwa na kungiyar APC X Eagle forum ya...

Yanzu-yanzu: Naja’atu Muhd ta mayarwa da Nuhu Ribado Martani Kan barazanar da ya yi mata

Daga Isa Ahmad Getso   Yar gwagwarmayar nan Hajiya Naja'atu Muhammad...

Zargin Sharrin: Ribado ya yi barazanar maka Naja Muhammad a Kotu

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Mai baiwa shugaban kasa shawara kan...

Rusau: Kwankwaso ya bukaci gwamnan Kano ya biya diyyar mutanen da aka kashe a Rimin Zakara

Daga Abdullahi Shu'aibu Hayewa   Jigon jam’iyyar APC a jihar Kano,...