Daga Safyan Dantala Jobawa
30/05/2022
An ja hankalin iyaye kan su san idanu akan yaransu bayan sun yi saukar Alkur’ani maigirma.
Sakataren ilimi na karamar hukumar Garun mallam Alh Sani Mato shi ya yi kira a cikin jawabinsa a taron bikin saukar Alkur’ani na makarantar Hidayati ‘Dalib kofar Fada Yadakwari da ke karamar hukumar Garun mallam.
Sakataren Ilimin yace akan sami dalibai mahadda da kan jefa kansu cikin mugayen dabi’u a sakamakon mu’amalla da bata garin abokai wanda hakan ke sanya rayuwarsu cikin mugun yanayi.
Don haka ya kalubalanci iyayen yara da sakacin lura da tarbiyya’ya’yan su bayan sun sami ilimin addini da ma na zamani.
Shi kuwa malam Adamu Abdullahi Kano tsokaci ya yi na cewe matukar iyaye Kan sun hani ‘ya’yan su mata abubuwa guda uku, na daya rike manyan wayoyi da yin mugayen kawaye da kuma samari barkatai wanda ya ce “ya zaman ruwan dare a cikin al’umma.
Wakilin Kadaura24 ya ruwaito mana cewar a wannan shekarar makarantar da Hidayati ‘Dalib ta samu damar yin saukar dalibai 45 a karo na 6, inda maza 17 sai kuma mata 28 a ka yi wa saukar.A wajen biki saukar ta bana maigirma shugaban karamar hukumar Garun mallam Alh Mudansur Aliyu Dakasoye ya bada tallafin naira dubu 200000 tare da alkarin inganta makarantar sai kuma tsohon danmajalisar jiha Hon Abdullahi Maikano Chiromawa ya bada nasa tallafin na naira dubu 50 nan take.
Sa’annan makarantar ta mika kyaututtukan yabo da girmamawa ga wasu manyan mutane da ke hidimtawa makarantar ba dare-ba-rana wadanda suka hadar da shugaban manoma tumatir na jihar Kano Alh Danladi Sani Yadakwari da dagacin yadakwari Alh Danayanu da dai sauran wsu fitattun manyan garin.
A karshe Ajiyan Rano kuma hakimin Garun mallam Alh Lawan Abubakar Madaki ya yaba da kwazon malamai da iyayen yara abisa irin namijin kokarinsu a wannan makarantar. Kana ya kuma bukaci iyaye da malamai su cigaba da nuna kyawan dabi’u da samun al’umma ta gari.
Daga bisa shugaban makarantar Malam Waisu Yadakwari ya godewa iyaye bisa tallafin da suke basu yau da kullum.
Mahalarta bikin saukar a wannan shekarar sun hadar da Alh Salmanu Kura da Dagacin Garun mallam Sani Tukur da Danmasani Garun mallam Abdurrahaman Tsoho sai shugaban kungiyar matasan karamar hukumar Garun mallam Alh Awaisu Umar Garun mallam da dai sauran mutane daban-daban na ciki da wajen karamar hukumar Garun mallam