Daga Mubaraka Aliyu Ibrahim
Magoya bayan Sanatan Kano ta Arewa Sanata Barau I Jibril sun yabawa dattako da yakanar gwamnan Jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje bisa janyewa da yayi daga takarar Sanatan Kano ta arewa.
Kadaura24 ta rawaito Mai baiwa Gwamnan Kano shawara akan harkokin al’umma tun daga tushe Hon. Yusuf Aliyu Tunfafi Wanda gudana ne cikin na hannun dama ga sanata Barau shi ne ya bayyana hakan yayin Wani taron Manema labarai a Kano.
Yace janyewar da Gwamna Ganduje ya yiwa Barau ya tabbatar da kishinsa ga al’ummar da Kuma kokarinsa na fifita bukatun al’umma akan tasa.
” Da Wannan abun alkhairin da Gwamna Ganduje ya yi ya tabbatar da cewa jam’iyyar APC zata Sami nasara tun daga sama har kasa, Saboda Wannan kokari ya nuna hakin kan ‘ya’yan jam’iyyar APC a yankin kano ta kano ta arewa da kano baki daya”. Inji Tunfafi
Hon. Yusuf Tunfafi ya kuma Kara da cewa sulhun da aka Samu tsakanin tsohon Kwamishinan Ma’aikatar Kananan Hukumomin Jihar Kano Murtala Sule Garo da Sanata Barau I Jibril, ya kara hade kan ‘ya’yan jam’iyyar APC baki daya.
” Sanata Barau Jibril ya yi aiyukan alkhairi da dama a yankin kano ta Arewa ta fuskar kawo gine-ginen makarantu da Asibitoci da Kuma samar da aikin yi ga matasa da Kuma ba da jari ga al’umma maza da Mata “. Inji Yusuf Tunfafi
Hon. Tunfafi ya kuma bada tabbacin Sanata Barau Jibril da Nasiru Yusuf Gawuna da sauran kujerun baki daya, Saboda abun arzikin da Suka yiwa al’ummar Jihar Kano.