Daga Yakubu Abubakar Gwagwarwa
Dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Wudil/Garko, Honarabul Muhammad Ali Wudil bayan ya zama dan takarar jam’iyyar APC a zaben 2023 mai zuwa ya Kuma godewa wakilan da suka gudanar da zaben har ya Sami Wannan nasara.
Kadaura24 ta rawaito Muhammad Ali Wudil wanda ya hau kujerar har karo na hudu a matsayin wanda ya lashe zaben fidda gwani ba tare da hamayya ba.
Da yake sanar da Sakamakon zaben zaben sakataren kwamitin zaben fidda gwanin Malam Isa ya bayyana cewa a Karamar Hukumar Garko wakilai 50 ne suka kada kuri’a kuma delegates 45 sun zabi Muhd Ali wudil yayin Kuma da kuri’u 5 suka lalace .
Ya kara da cewa, wakila 48 ne Suka zabi Muhd Ali daga Karamar Hukumar sa ta Wudil, yayin kuma da kuri’u 2 suka lalace . A cewarsa, an bayyana dan majalisar mai ci a matsayin wanda ya lashe zaben saboda babu wani dan takarar da ya shiga takara da shi.
Dan Majalisar ya godewa dukkanin masu ruwa da tsaki Waɗanda suka taka rawa wajen Samun nasarar lashe zaben fidda gwanin a Karo na biyar .
“Ina godiya ga Shugabannin Kananan Hukumomin Wudil da Garko da Masu girma Delegate da suka aminta da Chanchanta ta Suka Kara bani dama domin in yiwa jam’iyyar APC takara a Karo na biyar” inji Muhd Ali wudil
Da nasararsa, Ali Wudil zai tsaya takarar neman kujerar a karo na biyar. Rahotannin sun tabbatar da cewa an gudanar da zaben fidda gwanin lami Lafiya ba tare da Wani hargitsi ba.