Tsohon gwamnan Jihar Kano kuma dan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar NNPP, Rabiu Kwankwaso, ya musanta sayar da wakilan zaɓe na Kano ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP, Nyesom Wike.
Duk da cewa a na zargin shugabancin PDP, ƙarƙashin jagorancin Shehu Sagagi a jihar Kano na biyayya ga Kwankwaso, amma Kadaura24 ta tattaro bayanai cewa ba a baiwa Kwankwaso kuɗin da a ke raɗe-raɗin an bashi ba, wakilan a ka baiwa.
Wata kafar yaɗa labarai ce ta yi zargin cewa Wike ya sayi wakilan Kano 45 da za su halarci babban taron zaɓen ɗan takarar shugaban kasa na PDP kan dala 15,000 kowanne.
Sai dai kuma Kwankwaso, a wata sanarwar da hadiminsa, Ibrahim Adamu ya fitar a jiya Asabar domin mayar da martani a kan rahoton, ya suffanta rahoton a matsayin ƙarya da kuma yarfe.
Ya ce ” Abu ne sananne cewa, a ranar 29 ga Maris, 2022, Mai Girma Sanata Mohammed Rabiu Musa Kwankwaso ya yi murabus daga jam’iyyar PDP tare da yin jawabi ga taron manema labarai na kasa kan hakan. Don haka shirme ne ma a ce dan takarar shugaban kasa zai zai bauwa shugaban jam’iyyar adawa da kudi domin ya sayi wakilan jam’iyyarsa.
“Muna ma su musun ta wannan zarge-zargen gaba dayansa kuma muna kira ga jama’a da su yi watsi da shi a matsayin wani launi na tunani na wata jaridar yanar gizo. Don haka muna ba wa jaridar nan sa’o’i 48 da ta cire labarin na na karya tare da bayar da hakuri a cikin jaridu uku na kasa.
“A kan wannan batu na sama, muna kira ga jama’a da su yi watsi da bayanan karya domin kwata-kwata karya ce kuma an yi ne domin rikitar da al’umma,” in ji sanarwar.