Faduwar Tankar Mai Tayi Sanadiyar Jikkata Mutane 72 a Kano

Date:

Daga Nasiba Rabi’u Yusuf

Akalla Mutane 72 ne suka samu raunuka daban-daban a wata gobara da ta tashi da Maraice ranar Asabar din nan a gidan Man Fetur na Al-ihsan dake Sharada Phase 1, a Karamar Hukumar birni da Kewaye.


 Da yake ganawa da Jaridar News Watch Babban Sakatare, Kungiyar Red Cross ta Najeriya, reshen Jihar Kano Alhaji Musa D Abdullahi ya ce lamarin ya faru ne lokacin da wata tankar dakon Man Fetur ta kama da wuta.


 Ya ce kungiyar agajin gaggawa ta Red Cross ba tare da bata lokaci ba ta kwashe wadanda abin ya shafa 72 zuwa Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano don kula da lafiyarsu.
 ”Masu ba da agaji na Red Cross 7 sun halarci wajen Kuma sun Yi aikin sosai.


 “Lamarin ya rutsa da wasu ma’aikatan hukumar kashe gobara.”


 “Kamar yadda nake magana da ku yanzu wadanda abin ya shafa sun sami kulawar Ma’aikatan Lafiya”.

294 COMMENTS

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Tsofaffin Kansiloli Sun Yi Saukar Alƙur’ani da Addu’a na Musamman ga Gwamna Abba

  Ƙungiyar tsofaffin kansiloli na jihar Kano ta gudanar da...

Hisbah ta kama mutane 25 bisa zargin shirya auren jinsi a Kano

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama akalla mutane...

Yadda ƴansanda suka kama wasu da suke zargin ƴanbindiga ne a Kano

Rundunar yansanda ta Kasa reshen jihar Kano ta ce...

Rikici a Bebeji: Jigon Kwankwasiyya na zargin an shirya cire sunayen tsoffin kansiloli domin yin kashe-muraba

Wani jigo a tafiyar Kwankwasiyya a karamar hukumar Bebeji...