Daga Nafi’u Dansalo
Gwamnonin da aka zaba a karkashin jam’iyya mai mulki ta APC sun ce mambobin jam’iyyar daga kowane bangare na kasar nan suna da ‘yancin tsayawa neman kowane irin mukami a babban zaben na Shekara ta 2023.
Rikici na neman kunno kai a cikin APC kan yadda ake rarraba mukamai tsakanin Arewa da Kudu da kuma musamman shiyyoyi don samar da dan takarar shugaban jam’iyya na Kasa da shugaban kasa.
Amma a wata sanarwa a ranar Juma’ar nan a Abuja, shugaban kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC kuma gwamnan jihar Kebbi, Sanata Atiku Bagudu, ya ce jam’iyyar na Kara samun ci gaban.
“APC ta dukkan‘ yan Najeriya ce Kowane mutum, daga kowane yanki na ƙasar nan, yana da ‘yanci ya nemi kowane irin matsayi a cikin jam’iyya dai-dai da tanade-tanaden kundin tsarin mulkin jam’iyyarmu da kuma Tsarin Mulkin Nigeria na 1999.
“Jagoran falsafa kamar yadda yake kunshe a cikin Manufofin da muka gabatar su ne cigaban tattalin arziki, zamantakewa da siyasa na Najeriya.
“A matsayin na Gwamnonin Jam’iyyar APC, za mu ci gaba da tsayawa tsayin daka wajen tallafawa kokarin da kudurorin Shugaban kasa don gina jam’iyyarmu ta APC, a matsayin jam’iyyar siyasa mai karfi da dimokiradiyya a kasar Nan.
“Jam’iyyarmu ta APC, a bude take, a bayyane take kuma za ta ci gaba da ba da tabbacin yin takara cikin adalci a siyasa ga kowa, daidai da irin gagarumar sadaukarwar da Shugaba Muhammadu Buhari da dukkan shugabanninmu suka kafa.
Gwamnonin sun ce “Tare da zuwan Mr Ayade, karfin da jam’iyyarmu za ta yi wajen tattara duk wasu masu kishin kasa da sauran ‘yan Najeriya masu ra’ayin ci gaba zuwa APC Zai Kara karfinta.”