Yajin Aiki: Yi maza ka Zo ka kamani – Wabba ya fadawa El-Rufa’i

Date:

Shugaban kungiyar kwadago ta kasa (NLC), Ayuba Wabba, ya kalubalanci gwamnan jihar Kaduna, Nasir El’rufai, wanda ya bayyana cewa yana neman shi Ruwa a jallo Saboda kiran yajin aiki da yayia jihar, da cewa ya zo yasa a kamo shi.


 Shugaban NLC ya ce, “bari gwamna ya zo ya kama ni” yayin da ya jagoranci ma’aikata don zanga-zangar lumana a babban birnin jihar.
 Shugaban NLC ya kalubalanci El-Rufai, ya jagoranci masu zanga-zanga zuwa gidan gwamnatin Kaduna.


 An bayyana shugaban Kungiyar Kwadago a Matsayin Wanda ake nema Ruwa a jallo, in ji El-Rufai.


 Da yake ganawa da Manema a Kaduna yayin da yake jagorantar dubban ma’aikata, Wabba ya ce, “yajin aikin ba ana yinsa bane Saboda da ni.”
 “Bari ya zo ya kama ni.  Muna nan muna jiransu, ”in ji Wabba.


 Daily trust ta lura a yayin zanga-zangar cewa ma’aikatan da ke yajin aikin sun toshe babbar hanyar da ke cikin garin, inda suka tilasta wa masu ababen hawa komawa wasu hanyoyi.  Suna ta Daga alluna dauke da rubutu daban-daban.


 Gwamnan a safiyar yau Talata ya bayyana Wabba da sauran shugabannin kwadagon da ake nema saboda zargin zagon kasa ga tattalin arziki, tare da sanya lada ga duk wanda ya samu labarin inda suke.


 Wabba, duk da haka, ya jagoranci jerin gwanon ma’aikata zuwa gidan gwamnati, inda ya jajanta wa gwamnan da ya kama su.


 Kadaura24 ta rawaito cewa Bankuna, asibiti, tashar jirgin kasa, filin jirgin sama sun kasance a rufe yayin da jihar ta kasance cikin duhu yayin da ma’aikatan wutar lantarki suma suka shiga cikin yajin aikin .


 Wabba ya jaddada cewa kungiyar kwadagon ba za ta yi kasa a gwiwa ba har sai gwamnan ya amsa bukatun ta.


 NLC da rassanta sun shiga yajin aikin gargadi na kwanaki biyar a jihar don tilasta wa gwamnatin jihar ta sauya shawarar da ta yanke kan korar ma’aikatan jihar sama da 7000 a jihar ta kaduna.

168 COMMENTS

  1. Shi gwamna da yake irin wannan mugun halin bai San cewar raba mutum da aikin sa kamar kashe shi ka Yi ba, kamar yadda ba ya son rabuwa da kujerar sa haka ma’aikata suma ba sa son rabuwa da aikin su, wani sama da mutane goma yake ciyarwa, in ka kore shi kayi Yaya da wadannan mutanen, Kuma kar yadda kake Dan kaduna suma Yan kaduna ne. Aiki suke Yi ake ba su hakkin su. Tun hawan sa Karan tsana da ya sakawa ma’aikata yasa Garin shi babu zaman lfy, ya kasa magance matsalar sannan zai karawa jihar rashin zaman lfy, Muna goyon bayan wannan yajin aikin domin a nuna masa cewar sai ma’aikatan sun yi aiki sannan tattalin arzikin jihar zai samu, in Kuma Yana ganin shi da magoya bayan sa za su iya ga fili ga Mai doki Nan.

  2. Британец Энтони Джошуа и украинец Александр Усик 25 сентября 2021 года проведут бой в Лондоне. «МК-Спорт» решил узнать, а что об этом противостоянии думаю зарубежные эксперты. Александр Усик Энтони Джошуа 25.09.2021 «В андеркарді бою Джошуа – Усик ми хочемо влаштувати повернення Каллума Сміта в рамках напівважкої ваги. Крім того, відбудеться бій албанця Флоріана Марку та українця Максима Продана.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...