Yanzu-Yanzu:Kwankwaso ya je Fadar Sarkin Kano Don Ta’aziyyar Mai Babban Daki

Date:

Daga Muhd Kabir Diso

Tsohon Gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya Ziyarci fadar Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero domin yiwa Sarkin ta’aziyyar rasuwar Mai Babban Daki.

Sanata Kwankwaso ya Ziyarci fadar Sarkin da safiyar Talatar nan,tare da rakiyar Wasu Daga Cikin Magoya bayansa.

In dai Dade ana ta gunaguni aka Rashin ganin Madugun na kwankwasiyya a wajen jana’iza da Kuma lokacin da ake gudanar da Zaman makoki a fadar Sarkin.

Dama dai Wasu sun yi ta fadin cewa Kwankwason ba Zai je ta’aziyyar ba, Saboda abun da suke ganin Kamar Sanata Kwankwaso Bai yadda da tsarin da aka bi ba wajen raba Masarautar Kano da gwamnatin jihar Kano tayi.

Kadaura24 ta rawaito Lokacin da Mahaifin Kwankwaso ya rasu Sarakunan Kano da Bichi da Sauran sabbin Sarakunan Jihar Kano sun je yiwa Kwankwaso ta’aziyya .

Wannan ziyarar ta’aziyya da Kwankwaso ya kaiwa Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero ta Kawo Karshen Duk wani kace-nace da ake yi musamman a kafafen sadarwa na zamani.


Yayin Ziyarar Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso yayi addu’ar Allah ya gafartawa Mai Babban Dakin ya Sanya aljanna ta zamo makomarta.

98 COMMENTS

  1. Allah yaji kanta yayi mata rahama da duk al,ummar musulmi da suka rasu she kuma allah ya kara masa Lpy da tausayin talaka muna jin dadi wannan jaridar sako daga Khamisu hassan daga dubai

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...