Kamfanin S I da hadin gwiwar wasu gidajen Rediyo a Kano sun koyawa Matasa 500 sana’o’i

Date:

Daga Rukayya Abdullahi Maida

 

Dan Majalisa Mai Wakiltar karamar hukumar Birni a Majalisar wakilai ta kasa Hon. Sha’aban Ibrahim Sharada ya bayyana Kananan sana’o’i da cewa su ne ginshikin duk Wata babbar sana’a a duniya.

Sha’aban Sharada ya bayyana hakan ne lokacin taron yaye dalibai 500 da aka koyawa sana’o’in domin su dogara da kawunan, wanda kamfanin SI media hadin gwaiwa da gidan Radio Guarantee da express radio a jiya Asabar.

Dan Majalisar yace mafi yawan manyan masu kudi musamman yan kasuwa sun fara ne da Kananan sana’o’i har suka kai matakan da suke kai a halin yanzu.

Yace muddin masu kanana sana’o’i suka rike sana’o’in su da muhimmanci babu shakka zasu kai Matakin da basa tsammani, Kuma Idan mutum ya raina sana’ar babu shakka zai tsinci kansa Cikin dana sani .

“Matasa kune kashin Bayan cigaban al’umma don haka ku maida hankali wajen inganta sana’o’in da kuka koya don ku inganta Rayuwar ku data yan uwanku”. Inji Sha’aban Sharada

Ya Kara da cewa galiban matasa Raina kananan sana’oin da su keyi ne yasa ake barin su a baya.

Anashi jawabin shugaban kammfanin SI media Safwan Suraj Iliyas godiya yayi ga Allah daya nuna masa wannan Rana, kana Kuma yayi amfani da damar wajen kira ga mahukunta, kungiyoyi, da Kuma Dalibai dasu tashi tsaye don su taimaki marayu da masu rangwaman gata .

Kazalika ya Kara da cewa kamfanin nasa da taimakon gidan radio guarantee da express radio sun bada gudunmawa ga matasan Dalibai Maza da mata ta hanyar koya musu mabanbantan sana’oin don ganin sun Dogara da kansu.

Malama Amina muhd na daga cikin malaman da sukayi hidimar koya wasu daga cikin nau’ikan sana’oin ta bayyana wa kadaura24 cewa tayi matukar farin ciki da ganin wannan Rana da suke yaye Dalibai 500 daga cikin dubu guda da suka koyi sana’oin, irinsu dinka zanen gado, kwalliya, dinki, hada Sola, gyaran waya da sauransu.

A bangaren Wasu daga cikin daliban da suka rabauta da tagomashin koyon sana’ar da suka koya kyauta, sun bayyana farin cikinsu gami da fatan Alkhairi ga jagororan kamfanin SI media.

Taron dai ya samu halartar mutane da dama irinsu shugaban Samar da Ayyukan yi na Jihar Kano Mal. Idris Yakasai, Shugaban hadaddiyar kungiyar Yan Tifa na kasa reshen jihar Kano kwamarad Mamunu Ibrahim Takai, Hon. Sha’ban Ibrahim Sharada da sauran manyan baki da dama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Ba zaben 2027 ne a gaba na ba – Tinubu

    Fadar shugaban Najeriya ta bayyana cewa shugaba Bola Tinubu...

Rikicin Masarauta: Gwamnatin Kano ta Bayyana Matsayarta Kan Hukuncin Kotu

Daga Rukayya Abdullahi Maida   Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano kuma...

Da dumi-dumi: Gwamnan Kano ya tura tawaga mai karfi wajen Abba Ganduje

Daga Rahama Umar Kwaru   Babban Daraktan Hukumar Samar da Wutar...

Wata sabuwa: Sanata Barau Jibrin ya gana da Baffa Bichi da Muhd Diggol

Tsohon sakataren gwamnatin Jihar Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi...