Ba mu ji dadin abun da ‘yan Jaridu su kai mana ba – Inji Kwamishinan Shari’a na Kano

Date:

Fatihu Yusuf Bichi..

Kwamishinan shari’a na jihar Kano Barista MA Lawan ya ce nasarar da kungiyar ‘yan Jaridu ta kasa reshen jihar Kano ta samu akan rassan ma’aikatar guda biyu Abu ne na takaici da Sam shi da Lauyoyin da Ma’aikatan ma’aikatar basuji dadin sa ba..

Kadaura24 ta rawaito Kwamishinan ya bayyana hakan ne Jim kadan da tashi daga wasannin da aka fafata na kwallon kafa a gasar MAKON SHARI’A da ma’aikatar shari’ar jihar Kano ta shirya..

Barista MA Lawan yace an shirya wasannin ne domin sada zumunci da yin Nishadi tsakanin Ma’aikatar da sauran hukumomi da kungiyoyin da ke aikin Al’umma irin wadannan..

Ya kuma yabawa hukumomi da kungiyoyin da ke halartar gasar da aka fara a yau Asabar Kuma za’a karkareta a ranar Lahadi 20 ga watan nan na maris har ma ya bukaci Al’ummar jihar Kano su halarci wasannin da zaa karkare dasu a ranar ta Lahadi..

A wasannin na yau dai Kungiyar ‘yan Jaridu ta kasa reshen jihar Kano (NUJ)ta samu nasarar doke Kungiyar Lauyoyi ta kasa reshen jihar Kano (NBA)a wasan Farko da ci 2 da 1,,Sai Kuma wasa na biyu da NUJ ta buga da Kungiyar Ma’aikatan Shari’a(JUSUN)shima Yan Jaridar sun doke su daci 4 da 3 lamarin daya baiwa NUJ damar zuwa wasan karshe da zaa fafata ranar Lahadi..

Kungiyar Injiniyoyi ta kasa reshen jihar Kano da kungiyar Ma’aikatan hukumar kula da filaye ta jihar Kano Kangis da kungiyar likitoci na cikin kungiyoyin dake halartar gasar…..

Dama dai duk Shekara Kungiyar Lauyoyin ta Kasa takan Shirya tarukan makon Shari’a domin yin muhimman abubun da suka shafi harkokin Shari’a a Kasar nan

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta koka da kalaman mataimakin gwamnan Kano

Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozoma ta Najeriya (NANNM) reshen...

Kotu a Kano ta hukunta masu shago saboda zubar da shara a kan titi

Kotun tafi da gidanka da ke Kano ta yanke...

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kama mata da maza da ke aikata badala

Hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama mata hudu...

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Magantu Kan Batun Sheikh Abduljabbar

Hukumar Gyaran Hali ta Jihar Kano ta bayyana cewa...