Daga Abubakar Sa’eed Suleman
Mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhd Sa’ad Abubakar III ya bayyana cewa Majalisar da bata samu sahihin labarin ganin watan Shawwal a Duk fadin Nigeria ba.
Cikin Wata sanarwa da Kadaura24 ta samu Mai dauke da sa hannu Shugaban Kwamitin harkokin addinin Musulunci na fadar Sarkin Musulmin Farfesa Junaid wali ta bayan duban da aka yiwa watan ba a gan shi ba a Wannan rana ta Talata .
Sanarwa tace tunda ba’a ga watan ba Ranar Alhamis ita ce zata zamo Ranar 1 ga Watan Shawwal 1442 Ranar Sallah Karama kenan.
Sanarwa tace za’a gudanar da Azumi 30 Kenan a bana, Sarkin Musulmi yayi fatan Allah ya karbi ibadunmu ya Bamu lafiya da Zaman lafiya