Yan Social media abokan Aikin mu ne wajen cigaban al’umma – Shugaban K/H Kura

Date:

Daga Safiyanu Dantala Jobawa

Shugaban Karamar Hukumar Kura Mustapha Abdullahi Rabi’u ya bayyana gamsuwarsa da irin muhimmiyar rawar da Yan social media ke taka wa wajen cigaban aiyukan da shugabannin Kananan Hukumomi su ke aiwatarwa.


 Kadaura24 ta rawaito Shugaban karamar hukumar ta Kura ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karbi bakuncin ‘ya’yan kungiyar social media na karamar hukumar Garun Mallama gidansa da ke garin Kura don ta ya shi yin Murnar buda baki a yammacin ranar litinin nan da gabata.


Hon. Mustapha ya bada tabbacin yin aiki da su kafa-da-kafa a ko’ina don yada muhimman aiyukan da karamar hukumarsa ta ke yi a Sako da lunguna na Karamar Hukumar.


 Daga nan, ya Sha alwashin ganin ya taimaki kungiyar duk likacin da bukatar hakan ya taso, kuma ya gode wa kungiyar  social media ta Karamar Hukumar Garun mallam bisa irin wannan ziyarar da suka kai masa don Kara sada zumuncin juna.


Hon Mustapha ya gargadi ‘ya’yan kungiyar da su kiyaye doka da Oda a ya yin da suke gudanar da ayukansu don kaucewa hada wata fitina a tsakanin al’umma. 

 
A Jawabinsa tun da fari, jagoran ayarin Shugaban kungiyar social media ta Garun mallam, comrade Ahmad Isa Bagio Garun mallam, ya ce “sun kawo masa ziyarar ne don Kara kulla zumuncin da ke tsakanin al’ummar Kura da Garun mallam wanda suka gada tun tuni.

 
Daga nan, sun gode wa shugaban karamar hukumar ta Kura a bisa irin kyakkyawar tarbar da yayi musu . A karshe, shugaban kungiyar social media na karamar hukumar Kura, comrade Mahmud Aliyu Danhassan wanda shi ne mai masaukin baki, ya bukaci sauran Yan social media a duk inda suke da su Yi koyi da irin wannan don kara sada zumunci. 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Rundunar yansanda ta kasa ta aiko sabon kwamishina Kano

    Hukuamr Ƴansanda ta Najeriya ta amince da naɗi CP...

Yadda akai na bukaci Tinubu ya sauya sunan FCE Kano zuwa sunan Maitama sule

Daga Rahama Umar Kwaru   Mataimakin shugaban majalisar dattawan Nigeria Sanata...

Shugabannin hukumar zakka ta Kano sun ziyarci Sarki Sanusi II

Daga Sani Idris maiwaya   An bukaci Hukumar Zakka da Hubusi...

Nimet ta bayyana jihohin da za su fuskanci tsananin zafi

Hukumar kula da yanayi ta Najeriya ta yi gargaɗin...