Daga Sajida Ahmad
Majalisar dokokin jihar Kano ta musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa ta fara yunƙurin tsige shugaban majalisar Rt Hon Hamisu Ibrahim Chidari da mataimakin sa Hon Hamza Massu.
Shugaban masu rinjaye na Majalisar Hon. Labaran Abdul Madari ne ya bayyana hakan Yayin wata ganawa da yayi da gidan Radio Aminchi dake kano.
Madari yace basu da masaniyar wani yunkuri na tsige Shugaban Majalisar,Kuma yace labarin ba shi da tushe ballantana makama.
“Mun yanzu Muna Abuja ma dukkanin mu har da Shugaban Majalisar Rt. Hon. Hamisu Ibrahim chidari Inda Muka zo Rantsar da Shugaban jam’iyyar APC na Jihar kano Abdullahi Abbas Dan sarki jikan Sarki”. Inji Madari
Shugaban Majalisar yace Suna da kyakykyawar mahimta a tsakanin su Kuma yace bai ma ga dalilin da zai sa a tsige Shugaban Majalisar ba.
Wasu rahotanni sun nuna dai sun zargi cewa Kwamishinan ƙananan hukumomi Murtala Sule Garo ne ya kitsa tsige shugabannin, inda ya baiwa shugaban masu rinjaye na majalisar Hon Labaran Abdul Madari umarnin gudanar da shirin.
Shugaban masu rinjaye na majalisar yace babu ƙamshin gaskiya ko kadan akan Zargin.
Ku saurari hirar mu dashi 👇