Babbar kotun Jihar Kano Mai lamba 14 ta kori karar da wani Dan kasuwa Mai Suna Sani Isma’ila ya shigar gabanta yana zargin Shugaban Hukumar Kare hakkin Mai saye da mai sayarwa Janar Idris Bello Danbazau Mai ritaya ya nemi na Goro a Wajensa tare Kuma da Zargin Jami’an Hukumar sun kama masa kayansa ba bisa ka’ida ba.
Alkalin Kotun Mai Shari’a Nasiru Saminu ya yi watsi da karar, Inda yace akwai Hukumar da take da alhakin bincike Kan harkokin da suka shafi cin hanci da rashawa.
Kotun ta Kuma bada Umarnin a Cigaba da ajiye Kayan Mai Kara Wanda dama man ja yake sayarwa a Kasuwar Galadima , Kuma dama Hukumar tace ta maka man ne saboda gurbataccene ake sayarwa al’umma.
Kadaura24 ta rawaito Barr. Abubakar Salisu Muhd shi ne lauyan Hukumar Mai saye da mai yace sun gamsu da yadda Shari’ar, Inda yace an kori Shari’ar ne Saboda rashin hujjojin da suka gabatar a gaban Shari’a.
Yace za a Cigaba da ajiye gurbataccen Man Jan har Lokaci da Hukumar dake da alhakin binciken karbar zargin na goron .