Buhari, El-Rufai, KADCCIMA sun karrama Dangote a kasuwar baje koli

Date:

Madina Salisu Dukawa
 Shugaban kasa Muhammadu Buhari da mai masaukin baki Gwamnan jihar Kaduna sun yabawa shugaban Rukunin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, bisa kwarin gwuiwar sa wajen habbaka Kasuwanci da kuma taimakawa al’ummar kasar nan.
 Mutanen biyu sun bayyana hakan ne a wajen bikin baje kolin na Kaduna karo na 43 wanda shugaban kasar ya Kaddamar a karshen mako.
 Wadanda suka shirya bikin baje kolin cibiyar Kasuwanci,ma’adinai da noma ta jihar Kaduna wato (KADCCIMA) ya kuma bayyana Dangote a matsayin wanda ya fi bayar da gudunmowa ga cigaban tattalin arziki da Kuma gudanar da aiyukan Jin kai ga al’umma ta karkashin Gidauniya Aliko Dangote.
 Shugaba Buhari, wanda ya samu wakilcin Ministan Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Otunba Niyi Adebayo, ya kuma ziyarci rumfar Dangote inda ya ce kasar nan na godiya da irin tallafin da rukunin Kamfanoni Dangote ke baiwa al’ummar Nigeria.
 Ya bayyana Aliko Dangote a matsayin abokinsa saboda irin gudunmawar da yake bayarwa ga tattalin arzikin Najeriya, tallafawa ayyukan gwamnati da na zamantakewa.
 Kamfanin Dangote shi ne mafi girma wajen daukar nauyin Kasuwar baje kolin ta kasa da kasa a Kaduna karo na 43 da a yanzu haka ta ke gudana mai taken: Sake damarar bunkasa tattalin arzikin Najeriya don yayi dai-dai dana sauka kasashen duniya.
 A Jawabinsa gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufia, ya ce gwamnatin jihar Kaduna na samar da yanayin da masu zuba jari masu zaman kansu kamar su Dangote za su je jihar Kaduna don zuba jari.
 Kamfanin Dangote ne ke da hannun jari mafi girma a Kamfanin Mota na Dangote Peugeot da ke Kaduna.
 Gwamnan wanda ya samu wakilcin kwamishinan kasuwanci, kirkira da fasaha, Farfesa Kabiru Mato, ya ce jihar ta samar da tsare-tsare na sada zumunta domin jawo hankalin masu zuba jari na gida da waje.
 Da yake jawabi a wajen bikin bude taron, Darakta Janar Usman Saulawa ya yaba da alakar da ke tsakanin rukunin Dangote da cibiyar KADCCIMA.
 “Rukunin Dangote alama ce ta duniya a duniyar kasuwanci da masana’antu hakanan zan iya  ƙarawa da cewa kowanne gida ana amfani da kayan Dangote, Sannan kuma an san Dangote da ayyukan jin kai ta karkashin gidauniyar Dangote,” inji shi.
 Ya ce kamfanoni daga Indiya, Pakistan, Morocco, Chadi, Senegal, Mali, Jamhuriyar Nijar da kuma Bangladesh suna halartar bikin baje kolin kasuwanci.
 Kamfanonin da ke halartar taron a karkashin masana’antun Dangote sun hada da Dangote Cement, Dangote Sugar, NASCON, da Dangote Taki.
 Sanarwar da Sashen Sadarwa na Kamfanin na Kamfanin Dangote ya fitar ta ce mahalarta taron da ke neman yin kasuwanci da duk wani reshen kamfanin na iya cin gajiyar irin wannan damar ta wani tsari na musamman a rumfar.
 Ta bayyana jihar Kaduna a matsayin daya daga cikin manyan jihohin da ake Amfani da kayan Kamfanin a kasar nan, idan aka yi la’akari da matsayinta na tarihi a matsayin hedkwatar siyasar Arewacin Najeriya.
 Ta ce sabon takin Dangote da ya zama abun so ga manoma za a iya Samun shi a rumfar Kamfani.
 Sanarwar ta kara da cewa, baya ga kayayyakin da ake siyar da su a kan farashi mai sauki tare da fakiti na musamman, ana kuma gabatar da kayayyakin kyaututtuka ga kwastomomi a rumfar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Subscribe

Mafi Shahara

Karin Wasu Labaran
Related

Dubun wani magidanci da ke da’awar bin mamata bashi a Kano ta cika

Daga Aminu Gama   Kotun shari'ar musulunci da ke zamanta a...

Abubuwan da aka tattauna tsakanin Peter Obi da Gwamnan Bauchi Bala Muhammad

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi ya ce a...

Yanzu-yanzu: Manjo Hamza Al-Mustapha ya koma jam’iyyar SDP

Daga Maryam Muhammad Ibrahim   Major Dr. Hamza Al-Mustapha ya shiga...

Inganta aiyukan hukumar zakka hanya ce da gwamnatin za ta bi don rage talauci a Kano – Sarkin Rano

Daga Kamal Yakubu Ali   Mai martaba sarkin Rano Amb. Muhammad...