Daga Umar Hussain Mai Hula
Jami’an Hukumar Kare hakkin Mai saye da mai sayarwa KSCPC sun samu nasarar kama gurbataccen sinadarin hada lemo na Tiara wajen katan dubu uku(5000) da kuma madarar Milky da Timatir da Kifin gwangwani a Kasuwar Singa.
Kadaura24 ta rawaito Daraktan kula da ingancin abinchi na Hukumar Tijjani jafaru ne ya jagorancin Jami’an Hukumar domin bankado gurbatattun kaya da Wasu Yan kasuwa Mara kishi suke sayarwa.
Tijjani jafaru yace Suna Zargin an tanadi kayan ne domin sayar da su a lokacin azumi Mai Zuwa lokacin da aka fi bukatar irin Wadancan kayan .
“Mun Sami nasarar Kama Kayan ne a Kasuwar singa, Kuma Kayan sun hadar da Sinadarin hada Lemo na Tiara kifin kwankwani Madarar Milky da Timatirin kwankwani Filawa da shinkafa. Kuma Muna Zargin an tanadi kayan ne domin sayarwa al’umma a lokacin azumi Mai Zuwa”. Inji Tijjani jafaru
Daraktan kula da ingancin abinchi ya Kuma yabawa al’ummar Jihar Kano bisa hadin Kan da suke baiwa Hukumar wajen basu bayanan Sirri domin dakile zagon kasan da Wasu yan Kasuwa suke yi wajen Shigo da Kayan marasa inganci a Jihar Kano.