Daga Sayyadi Abubakar Sadeeq
Kungiyar Kwararrun akantoci ta Kasa reshen Jihar Kano (ICAN) da hadin gwiwar Gidauniyar Yahaya kansila sun bukaci Yan Kasuwa a Jihar Kano da su sauka daga tsohon tsarin Kasuwanci Zuwa Sabon tsarin Amfani da masana a sha’anin Kasuwancinsu Kamar Yadda ake yi ko’ina a duniya.
Kadaura24 ta rawaito Shugaban gidauniyar ta yahaya kansila Dr. Usman Yahaya kansila shi ne ya bayyana hakan yayin taron bita ta yini guda wadda aka shiryawa Shugabannin Kasuwanni dake kano.
Dr. Yahaya kansila yace idan akai la’akari da yadda Kano take Cibiyar Kasuwanci a Arewacin kasar nan tun da dadewa, Akwai bukata Yan Kasuwa su zamanatar da sha’anin Kasuwancinsu domin su Rika Samun Riba Mai yawa da Kuma dakile yawan asara da Yan Kasuwar Kan yi.
Yace a sabon tsarin Kasuwanci ba a harkar kudade ba tare da masana ba, Waɗanda zasu Rika tsara yadda al’amuran kudade zasu kasance da lissafa su yadda ya dace tare Kuma da karbar shawarwari daga masanan domin rage yawan asarar da ake yi.
” Mun Shirya bitar ne Saboda mun fahimci yadda Kasuwanci a kullum suke Samun Koma baya a Kano, don haka muka ga ya dace mu Shiryawa Yan uwanmu Wannan bitar domin su fahimci muhimmancin Sanya Kwararrun lissafi da kididdigar kudaden Cikin Kasuwancin su don farfado da Kasuwancin”inji Yahaya Kansila
Yace a Karshen taron Suna fatan dukkanin mahalatta bitar zasu daina Kasuwanci a tsari irin na da da Rashin Ilimi, su Koma yin Kasuwancin su a Ilimance a zamance ita ce mafita ga Kasuwanci, tare kuma da bada damar daukar aiki ga Matasa yan kano da Suka karanci Ilimin akanta Kuma Suka kware.
tsahon Kwamishinan kudi na jihar kano Kuma Malami a Jami’ar Bayero dake Kano Farfesa Kabiru Dandago ya gabatar da makala a yayin taron bitar Mai taken Muhimmanci ajiye kididdigar lissafi ga ‘yan Kasuwa .
Yace idan yan kasuwa suka Sanya masana da zasu yi musu wannacan aiki zai taimaka musu wajen rage zurarewar kudaden da Kuma Samun damar amfanuwa da tallafi kala-kala da gwamnatoci suke bujiro da su don Bunkasa sha’anin Kasuwancin.
Wasu daga Cikin yan Kasuwar da Muka zanta da su sun baiyana Mana Jin dadinsu tare da bada tabbacin zasu yi Amfani da bitar don inganta harkokin Kasuwancinsu.
Taron ya Sami halartar Shugabannin Kasuwanni dake Kano da kwarrun akantoci da Sauran masana da dai Sauransu.