Daga Rukayya Abdullahi Maida
Tsagin su Malam Ibrahim Shekarau sun sake Fitar da Sabbin sharudda Sulhu da bangaren Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje domin Samun Sulhu tsakanin bangarorin biyu.
Kadaura24 ta rawaito Yan G7 din dai sun bayyana sabbin Sharuddan su Cikin Wata wasika Mai kwanan Wata 10 ga Wata fabarairu na Shekarar 2022 wadda aka aikawa Ofishin uwar jam’iyyar APC na Kasa mai dauke da sa hannun dukkanin Yan G7 din .
Sharuda dai guda 3 Waɗanda suka ce sai an Cika su Sannan zasu sake yadda da Zaman sulhun.
1. Muna Nan akan matsayarmu ta cewar za a bamu kaso 55 cikin 100 sannan a bamu shugaban Jamiyya, su Kuma bangaren Ganduje su dauki kaso 45.
2. Gwamna ba zai sake Jagorantar duk wani kwamitin sulhu ba saboda yana daga cikin Wanda ake rigima dasu.
3. Sai bangaren Gwamnati sun janye karar da suka Shigar a kotun daukaka kara. Yin hakan zai tabbatar cewa an shirya yin sulhu bisa adalci.
Wannan sune sharudan da aka turawa shugaban Jamiyyar APC ta kasa Kuma Gwamnan jihar Yobe Mai Mala Buni.
Idan za’a iya tunawa Kadaura24 ta rawaito Shugaban Kwamitin Rikon jam’iyyar APC na Kasa Mai Mala Buni ya aikowa da bangarorin biyu takardar yadda za a Sami Sulhu tsakanin su, Inda jam’iyyar ta dorawa Gwamna Ganduje jagorancin Kwamitin Rabon mukaman jam’iyyar, sai dai tsagin Yan G7 sun fatali da sanarwar.