Daga Zara Jamil Isa
Shahararren mawakin fulani nan, Ibrahim Abubakar wanda aka fi sani da M Pulanis Gombe ya fitar da sabon album dinsa mai suna Fulfulde Duuniya.
A cikin wata sanarwa da ya aikowa Kadaura24, tauraron Fulanin ya bayyana cewa sabon Album ɗin nasa za’a iya samunsa tare da sauke shi Kafafen sadarwa na yanar gizo.
Yace a Cikin faifan bidiyon ya baje kolin kyawawan al’adun Fulani a Afirka Wanda Zai kayatar da duk Wanda ya kalle shi, Sannan Kuma yayi Amfani da Kayan daukar sauti da daukar hoto na Zamani irin Waɗanda ake yayinsu a Duniya.
M Pulanis ya kara da cewa sabon kundi “yana zuwa ne bayan kabilar ‘Fulfulde/Pular tana fuskantar babban koma baya”.
M Pulanis Gombe dan asalin jihar Gombe ne a Arewacin Najeriya.
Gwamnatoci kasashe da yawa suna Amfani da harshen Fulatancin a Matsayin harshen kasa, kasashen sun hadar da Senegal, Guinea, Senegambia, Maasina (Nijar Delta ta ciki), Arewa maso Gabashin Najeriya, Kamaru, Mali, Burkina Faso, Gambia, Ghana ta Arewa, Kudancin Nijar da Arewacin Benin (a yankin Borgou, da harshen gida a yawancin kasashen Afirka, irin su Mauritania, Guinea-Bissau, Saliyo, Togo CAR, Chadi, Sudan, Somalia da Habasha, Akwai Mutane sama da miliyan 95 da magana da harshen Fulatanci a duniya.
A Najeriya ana amfani da yare a ko’ina, musamman a yankin Arewa, anfi Amfani da harshen a jihohin da aka Adamawa, Taraba, Bauchi, Gombe, Kano da dai sauransu.