Daga Nazifa Ahmad Sagagi
Shirin gina cibiyoyin tattara madarar madara guda 200 a jihar Kano da Shirin bunkasa noma da kiwo na jihar Kano, KSADP, sun kudirci aniyar inganta bangaren samar da Madarar shanu da nufin inganta rayuwa da makiyaya musamman mata.
Sanarwar da Shugaban yada labaran Shirin Ameen K Yassar Shugaban Shirin na KSADP, Malam Ibrahim Garba Muhammad ne ya bayyana haka a lokacin bude taron masu ruwa da tsaki kan cibiyoyin tattara madara, a Kano, inda ya bayyana cewa bankin ci gaban Musulunci da Asusun Raya al’umma LLF ne suka dauki nauyin aikin.
“Wannan wani muhimmin mataki ne na bunkasa harkokin madara wanda zai inganta Rayuwar makiyaya musamman mata, ta hanyar tabbatar da ingancin madara, tsafta da Kuma ribarta”.
“Da wannan ci gaban, wanda kuma zai haifar da alaƙa da Mata Masu sayar da nono da manyan ƴan wasa a harkar tattara madara da Kasuwancin ta, zai taimaka wajen rage wa Matan karkara wahalhalun da suke fuskanta na tafiyar Kasa da sayar da nono ba a farashi Mai rahusa”. Inji sanarwar
Ya ce idan aka inganta hanyoyin tattara madara da adanata da kuma Kasuwancin ta, makiyaya da gwamnati za su samar da ingantaa hanyar shiga da kuma taimakawa wajen dakile kashe kudaden da gwamnatin tarayya ke kashewa wajen shigo da madara daga kasashen waje.
Malam Ibrahim ya bayyana cewa daga cikin cibiyoyin tattara madara guda 200 da KSADP za ta gina, za a gina 40 tare da samar da kayan aiki a fadin kananan hukumomi 15 na jihar a bana.
Hajiya A’isha Muhammad Abubakar, shugabar mata ta MACBAN ta kasa, ta bukaci mata da su taka muhimmiyar rawa wajen tafiyar da harkokin MCC saboda irin rawar da ake takawa a harkar kiwo tun daga nono har zuwa kasuwa.