Daga Abubakar Sa’eed Suleman
Wani Matashi Mai kimanin shekaru 22 ya Rubuta Sunan Wata Yar wasan Hausa da wuka a hannun sa don ya nuna irin kaunar da yake Yi Mata.
Matashi Wanda ya rubuta Sunan Ummi Rahab yarinyar data taba fitowa Cikin wani Shiri fim Mai Suna “Ummi” fim din da acikinsa aka yi wakar “kin zamo takwara Ummi an rada Miki Suna,baba ka share hawayena …..”.
Matashin wanda yaki baiyana sunansa yace ya Rubuta Sunan jarumar ne Saboda da Tsananin kaunar da yake yi Mata.
Ummi Rahab dai yanzu tauraruwarta tana haskawa tun da tayi wani Sabon Shiri Mai dogon zango Mai Suna Farin Wata, Wanda hakan tasa take ta Samun masoya.
Kadaura24 tayi kokarin jin ta bakin Ummi Rahab Dangane da Wannan batu,Amma hakarmu Bata cimma Ruwa ba.
An Dade ana samun Mata da Matasa da suke aikata irin Wannan da Sunan Kauna ga Jaruman Kanywood Dama sauran wadanda Suka shahara.