Daga Rukayya Abdullahi Maida
Wani Mai Shirya fina-finan Hausa Mai Suna , Ali Sa’id ya ce a wata mai zuwa ne za a fara fim mai dogon zango mai taken “Hanifa” kan yarinyar da aka kashe a Kano.
BBC Hausa ta rawaito Ali Sa’id ya ce babban dalilinsu na yin fim din shi ne domin wayar da kan iyaye kan yadda za su saka ido kan yaransu bayan abin da ya faru da Hanifa.
“Muna kuma son a rika tunawa da Hanifa ta hanyar wannan fim din” a cewar mai shirya fim din.

Iyaye da dama sun nuna sha’awar wannan fim din kuma sun kawo yaransu domin fitowa a matsayin Hanifa a fim din.
Idan za’a tuna a makonni bayan ne dai Malamin su wata yarin Mai Suna Hanifa Abubakar ya sace ta kuma ya yi Mata kisan gilla a Kano,lamarin da ya dawo akai ta magarna a Kafafen yada labarai da shafukan Sada Zumunta.