Mai magana da yawun Shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ya bayyana cewa ƴan siyasa da dama a ƙasar sun zaƙu Shugaba Muhammadu Buhari ya kammala wa’adin mulkinsa na biyu domin su koma “gidansu na jiya” na wadaƙa da kuɗin al’umma.
Malam Garba Shehu ya bayyana haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya ce ƴan siyasan sun ƙosa su ci gaba da kwasar kuɗin al’umma suna kai wa asusun ƙasashen waje.
Ya bayyana cewa ƴan siyasa da dama ba sa ƙaunar a sake samun wani kamar Shugaba Muhammadu Buhari.
“Duk da cewa shugaban ƙasa zai sauka bayan an zaɓi wanda zai maye gurbinsa a shekara mai zuwa – ko da sabon shugaban zai ɗora kan kyakkyawan tsarin da ya kafa ko ba zai ɗora ba – ayyukan da ya yi suna da yawa kuma abu ne mai wahala a kawar da su,” in ji shi.
Garba Shehu ya lissafo wasu manyan abubuwa da Shugaba Buharin ya yi wanda yake ganin za a rinƙa tunawa da shugaban saboda su:
Ya ce kotuna sun yi adalci ga waɗanda aka gurfanar a gabansu duk kuɗin mutum duk talaucinsa, haka kuma ya ce an samu karɓo kuɗaɗen da aka sace shekaru da dama aka kai ƙasashen waje inda bayan an karɓo kuɗin an yi amfani da su wajen gudanar da ayyukan ci gaba ga talaka.
Haka kuma ya bayyana cewa shugaban ya kawo sauye-sauye da suka kawo sauƙi matuƙa ga rikice-rikicen da ake fama da su na ƙabilanci da aka shafe ɗaruruwan shekaru ana yi – kamar rikicin manoma da makiyaya.
Mai magana da yawun shugaban kasar ya ce wasu daga cikin ƴan siyasa na amfani da waɗannan rikice-rikicen ƙabilanci domin cimma wani buri nasu na siyasa.
Sai dai Garba Shehu ya bayyana cewa babbar nasarar da shugaban ya samu ita ce kawar da tunanin da jama’a ke yi cewa duka masu shugabancin Najeriya suna neman kujerar mulki ne domin azurta kansu da iyalansu da kuɗin gwamnati.
Ya ce Shugaba Buhari ya kawar da wannan tunanin kuma ƴan siyasa da dama na jin haushin hakan.
Gwamnatin Shugaba Buhari dai na shan suka daga ɗumbin ƴan siyasa a ƙasar da wasu daga cikin talakawan ƙasar inda suke kokawa da tsadar rayuwa da rashin tsaro.
Sai dai Shugaba Buharin ya sha fitowa yana cewa an samu sauƙi matuƙa a ɓangaren tsaro idan aka kwatanta da gwamnatin baya haka kuma kan batun tsadar rayuwa ya sha cewa gwamnatinsa ta samar da ayyukan yi da kuma inganta manoma da masana’antu.
Abubuwan da gwamnatin Shugaba Buhari ta sa a gaba tun a 2015 sun haɗa da yaƙi da cin hanci da rashawa, tabbatar da tsaro da kuma bunƙasa tattalin arziƙi.